'Yan Daba Sun Kaiwa Matar Gwamnan a Arewa Farmaki, An Halaka Mutum 1

'Yan Daba Sun Kaiwa Matar Gwamnan a Arewa Farmaki, An Halaka Mutum 1

  • Wasu 'yan daba a ranar Asabar sun farmaki tawagar matar Gwamna Ahmadu Fintiri, Lami Ahmadu Fintiri a jihar Adamawa
  • Sun tare tawagarta a garin Muchala da ke yankin Mubu inda suka yi musu ruwan duwatsu da sandu kafin su sha da kyar
  • Duk da matar gwamnan bata samu rauni ba, daya daga cikin 'yan tawagarta ya samu rauni a kai amma yana samun sauki

Yola, Adamawa - 'Yan daba a ranar Asabar sun farmaki tawagar matar gwamnan jihar Adamawa, Lami Ahmadu Fintiri.

'yan sanda
'Yan Daba Sun Kaiwa Matar Gwamnan a Arewa Farmaki, An Halaka Mutum 1. Hoto daga Thecable.ng
Asali: UGC

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin a takardar da ya saki ga manema labarai a Yola ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Bude Wa Ayarin Motoccin Dan Takarar Gwamna Wuta, Sun Bindige Direbansa

Yace an kai farmaki kan tawagar motocinta ne a garin Muchala da ke yankin Mubi inda wasy bata-gari suka dinga jifansu yayin da suka shiga wani kauye halartar taron matan Katolika.

'Yan daban da ke dauke da duwatsu da sanduna sun ragargaza mota kirar bas mai mazaunin mutum 18 da ke dauke da manema labarai kuma sun rauna wani mutum daya mai suna Dauda, Daily Trust ta rahoto.

Daya daga cikin wadanda ke cikin tawagar da baya so a kira sunansa saboda bashi da damar tattaunawa kan batun, ya sanar da Daily Trust cewa matar Fintiri bata samu rauni ba kuma bayan nan ta koma Yola yayin da Dauda da ya samu a rauni a kai yake samun sauki.

Takardar da 'yan sandan suka fitar ta ja kunnen masu tada fitina kan cewa ba za su ci banza ba saboda rundunar ta shirya tabbatar da zaman lafiya a jihar inda ta kara da cewa an aike jami'ai don cafko maharan.

Kara karanta wannan

Manya basu tsira ba: 'Yan bindiga sun tare motar kwamishinar mata, sun yi awon gaba da ita

Nguroje yace kwamishinan 'yan sandan jihar, SK Akande, ya aike da jami'ai daga rundunar SRRT don dakile abinda ka iya tasowa tare da cafko bata garin.

Matashi ya bindige sauryain kanwarsa

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wani matashi da ya harbi saurayin kanwarsa da bindiga.

An gano cewa, soyayyar shan minti suke yi kuma ya raba shi da kanwarsa amma ya ki ji, lamarin da yasa ya dauka hukunci a hannnunsa bayan da ya kama su dumu-dumu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel