Yan Bindiga Sun Bude Wa Ayarin Motoccin Dan Takarar Gwamna Wuta, Sun Bindige Direbansa

Yan Bindiga Sun Bude Wa Ayarin Motoccin Dan Takarar Gwamna Wuta, Sun Bindige Direbansa

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai wa Charles Otu, dan takarar gwamnan Ebonyi karkashin jam'iyyar APGA hari
  • Maharan sun yi fakin din motarsu ne a hanyar Enugu/Abakaliki inda suka jira tawagar Otu, suka bude wutar har sun kashe direba daya cikin tawagar
  • Otu, cikin sanarwar da ya fitar ya ce wasu yan sanda uku cikin masu tsaronsa sun jikkata kuma akwai wasu wadanda har yanzu ba a gansu ba

Ebonyi - The Punch ta rahoto cewa a daren ranar Alhamis ne wasu yan bindiga suka tare tawagar motoccin dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance a jihar Ebonyi, Bernard Odo.

Hadiminsa na bangaren watsa labarai, Charles Otu, ya tabbatar da harin, yana mai cewa dan takarar yana hanyarsa na dawowa ne daga kamfen a lokacin da yan bindigan suka tare shi a Rest House kan babban hanyar Enugu/Abakaliki.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Budewa Dan Takaran Gwamnan Jihar Ebonyi Wuta, An Kashe Direbansa

Taswirar Eboni
Yan Bindiga Sun Bude Wa Ayarin Motoccin Dan Takarar Gwamna Wuta, Sun Bindige Direbansa. Hoto: @VanguardNGR
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan bindigan, wadanda suka yi fakin din wata mota kirar Sienna a kan hanyar sun bude wa tawagar gwamnan wuta na nufin harbin gwamnan.

An rahoto cewa an harbi direban kuma an masa lahani sosai hakan yasa dan sanda mai tsaron ya yi kokarin ya fice da motar daga wurin.

The Nation ta rahoto cewa daga bisani direban ya riga mu gidan gaskiya saboda raunin da ya yi.

An tattaro cewa wasu yan sanda uku masu tsaron dan takarar gwamnan sun jikkata.

Ba wannan ne karon farko da ake kai wa Otu hari ba

Wannan shine karo na biyu da ake kai wa dan takarar gwamnan na jam'iyyar APGA hari bayan harin da aka kai masa a baya a karamar hukumar Izzi yayin da ya ke hanyar zuwa kamfe.

Kara karanta wannan

Karina Bayani: Gwamnonin APC Sun Roki Buhari Ya Bari a Dinga Amfani da Tsofaffi da Sabbin Kudi

Wadanda suka samu rauni suna asibiti ana musu magani a Abalaliki, babban birnin jihar.

Otu, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce har yanzu akwai wasu mutanen da ba a gansu ba bayan harin.

Ya kuma ce yan bindiga sun kona daya cikin motoccin da ke tawagar.

Yan bindiga sun kai wa jami'an tsaron fadar shugaban Najeriya hari

A wani labarin a baya, kun ji cewa wasu yan bindigan sun yi barazanar garkuwa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Yan bindigan da ba a san ko su wanene ba sun kai wa sojojin Gaurds Brigade harin kwanton bauna a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel