‘Yan Sanda sun Cafke Matashin da Ya Harbi Saurayin Kanwarsa a Ogun

‘Yan Sanda sun Cafke Matashin da Ya Harbi Saurayin Kanwarsa a Ogun

  • Wani matashi ya tsallake rijiya da baya yayin da yayan budurwarsa ya harbe shi gami da raunata shi bayan da ya ritsa su suna tsaka da ‘shan mint I’ da kanwarsa
  • Kamar yadda wanda ake zargin ya bayyana, ya dauki tsawon lokaci yana jan kunnen saurayin kanwarsa da ya rabu da ita amma ya yi kunnen uwar shegu
  • Sai dai, tuni aka garzaya da wanda lamarin ya auku da shi babban asibitin Idi-Iroko don ceto rayuwarsa, yayin da aka mika wanda ake zargin sashin bincike don gurfanarwa

Ogun - Jami'an 'yan sandan jihar Ogun sun yi nasarar cafke wani matashi mai shekaru 30 da ya harba gami da jima saurayin kanwarsa, Tobi Olabisi rauni bayan ya gano yadda suke ‘shan mint I’ da kanwarsa.

‘Yan sanda
‘Yan Sanda sun Cafke Matashin da Ya Harbi Saurayin Kanwarsa a Osun. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Lamarin ya auku ranar Juma'a a Idi-Iroko cikin karamar hukumar Ipokia ta jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karancin Mai Da Kudi: An Yi Kare Jini Biri Jini Yayin Zanga-zanga a Wata Jahar Najeriya, An Kashe Mutum Daya

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi ne ta sanar da hakan a wata takarda da ta fitar ranar Lahadi.

Oyeyemi ya bayyana yadda aka cafke wanda ake zargin bayan wani korafi da sarkin anguwar Ihunbo, Alpha Akeem ya shigar a hedkwatar 'yan sandan yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin ya ce, an shigar da korafi kan yadda aka raunata wani a ofishin, inda aka kai karar wanda ake zargin, jaridar TheCable ta rahoto.

A cewar Oyeyemi, Akeem wanda ya dade yana jan kunnen wanda lamarin ya auku da shi da ya daina soyayyar shan minti da kanwarsa, hakan yasa ya harbeshi, amma wanda lamarin ya auku da shi ya tsalleki mutuwa da baya.

Oyeyemi ya bayyana:

"Yayin da aka samu rahoton, DPO na Idi-Iroko, CSP Ayo Akinsowon, ya hanzarta hada tawagar bincike don kamo wanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Shekara 20 Mai Koyon Sana'a Ya Kashe Mai Gidansa, Ya Jefa Gawarsa Cikin Rijiya

"Yayin da aka kama shi, wanda ake zargin ya yi ikirarin jan kunnen wanda lamarin ya faru da shi kan ya rabu da kanwarsa amma ya yi kunnen uwar shegu.
“A bakar ranar da lamarin ya auku, ya samu labarin yadda wanda lamarin ya ritsa dashi da kanwarsa inda ya je wurin da bindiga.
"Lokacin da ya isa wurin, wanda lamarin ya faru da shi ya dira ta taga wanda hakan ne ya sa wanda ake zargin harbinsa.
"An garzaya da matashin babban asibitin Idi-Iroko inda ya ke samun kula."

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Lanre Bankole, ya yi umarni da hanzarta mika wanda ake zargi bangaren binciken kisan kai na sashin binciken laifuka don garfanar wa.

Magidanci ya kona matarsa saboda ta ki masa girki

A wani labari na daban, wani magidanci ya watsawa matarsa fetur tare da cinna mata wuta saboda ta ki yi masa girki.

Bayan da ‘yan sanda suka kama sh, ya sanar da cewa wankin kayansa ta tsaya yi shyasa bata yi masa girkin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel