Karin haske: ’Yan Sanda Sun Mamaye Gidan Gwamnan CBN da Ke Abuja

Karin haske: ’Yan Sanda Sun Mamaye Gidan Gwamnan CBN da Ke Abuja

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, rundunar 'yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta mamaye gidan gwamnan CBN
  • Wannan lamarin ya faru ne da daren yau Talata 17 ga watan Janairun 2023, inji rahoton fitacciyar jarida a Najeriya
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnan CBN Godwin Emefiele da jami'an tsaron Najeriya game badakalar kudi da ake zargin ya yi

Maitama, Abuja - A halin da ake ciki, wasu jami’an ‘yan sanda suna can a gidan gwamnan CBN, suna sanya ido saboda wasu dalilai masu karfi.

A cewar rahoton Punch, wakilin jaridar ya ga jami’ai sama da 10 na sintiri a gidan da misalin karfe 8:40 na dare a ranar Talata.

An ga suna ta kai komo ne a gidan gwamnan, Godwin Emefiele mai lamba 8 a titin Colorado da ke Maitama a Abuja.

Kara karanta wannan

Rudani: Ana dabs da zabe, an kama kakin soja da aka shigo dashi Najeriya

Gwamnan CBN ya shiga magana, 'yan sanda sun mamaye gidansa
Yanzu-Yanzu: ’Yan Sanda Sun Mamaye Gidan Gwamnan CBN da Ke Abuja | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Wata majiya mai karfi daga hukumar ‘yan sanda ta bayyanawa wakiilin jaridar cewa, sun mamaye gidan ne saboda ana kyautata zaton gwamnan zai bayyana a gaban kotu gobe Laraba 18 ga Janairu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce zai bayyana a gaban alkali ne don ba da bahasi kan wasu kudin da suka kai $53m da ke alaka da Paris Club.

Da take bayyana dalilin taruwan ‘yan sandan a gidan gwamnan, majiyar ta ce:

“’Yan sandan ba sun zo kama shi bane, sun zo ne don tabbatarwa bai gudu ba kamar yadda ya yi a makwannin baya.”

Rundunar ‘yan sanda ta magantu

Sai dai, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ta karyata cewa ta tura jami’an don mamaye gidan gwamnan na CBN.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan birnin, Olumuyiwa Adejob ya ce:

“Bani da masaniya game da wannan lamari. Amma, ku tuntubi rundunar FCT.”

Kara karanta wannan

Wata Mota Dauke Da Jarkokin Man Fetur Da Kama Da Wuta A Kano

A bangarenta, kakakin FCT, Josephine Adeh ya ce bata san da batun mamaye gidan Godwin Emefiele ba, kamar yadda jaridar ta fada.

A cewarta:

“Ban san komai game da cewa ‘yan sanda sun mamaye gidan gwamnan CBN ba. Ku tuntubi Hedkwatar rundunar.”

A jiya Litinin kunji yadda aka yada labarin cewa, gwamnan ya gamu da tsaiko yayin da DSS ta mamaye ofishinsa, amma daga baya aka ce ba gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel