Ba Mu Yi Mamaya a Babban Bankin Najeriya Na CBN Ba, Inji Hukumar DSS

Ba Mu Yi Mamaya a Babban Bankin Najeriya Na CBN Ba, Inji Hukumar DSS

  • Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi karin haske game da labarin da ke cewa, ta kama gwamnan CBN da yammacin yau Litinin 16 ga watan Janairu
  • An yada labarin yadda jami'an hukumar suka mamaye hedkwatar CBN tare da cewa suna son kama gwamnan bankin
  • Duk da yaduwar rahoton daga manyan jaridu a kasar nan, DSS ta ce sam bata yi hakan ba, ta yi karin haske a kai

FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta karyata rahotannin da ke cewa ta yi mamaya a ofishin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da ke birnin tarayya Abuja.

Godwin Emefiele ya shiga kanun labarai a Najeriya tun shekarar da ta gabata kann cewa hukumar tsaro ta DSS na farautarsa saboda wasu dalilai, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba a Afrika kadai bane: Kamar dai na ASUU, malamai a Ingila za su shiga yajin aiki

ayan gaza amsa gayyatar majalisar wakilai kan batun da ya shafi sabbin dokokin kudi na CBN, wakilansa sun ce tuni gwamnan ya tafi hutu kasar waje.

Hukumar tsaro ta DSS ta magantu kan batun mamaye CBN
Ba Mu Yi Mamaya a Babban Bankin Najeriya Na CBN Ba, Inji Hukumar DSS | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An ruwaito cewa, Emefiele ya dawo gida Najeriya a ranar Litinin 16 ga watan Janairu, kuma awanni kadan aka ce DSS ta mamaye ofishinsa domin kama shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma a cikin wata sanarwa, hukumar ta tsaron farin kaya ta karyata labarin tare da bayyana gaskiya abin da ke faruwa.

Abin da DSS ke cewa

Sanarwar ta ce:

"Hukumar tsaro ta farin kasa (DSS) ta samu labarin labaran karya da ke yawa suna cewa jami'anta sun yi mamaya a Babban Banckin Najeriya kuma sun kame gwamnata a yau, 16/1/23. Wannan labarin karya ne kuma mai batarwa."

A baya kunji yadda babbar kotu mai zama a Abuja ta ba da umarnin hana kama gwamna saboda wasu dalilai da ya bayyana, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rudani: Ta karewa gwamnan CBN yayin da jami'an DSS ta mamaye ofishinsa da yamma

Mai shari;a M.A Hassan ne ya ba da wannan umarnin a daidai lokacin da hukumar ta nemi a ba ta damar bincikar gwamnan.

A rahoton baya kunji yadda aka ce an ga jami'an hukumar DSS a cikin motoci sama da 20 lokacin da suka dura hedkwatar CBN.

Ana kyautata zaton sun zo kama gwamnan bankin kafin daga bisa bayanai su fito daga hukumar ta DSS, inda tace bata kama gwamnan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.