Gwamnan Babban Banki CBN Ya Dawo Najeriya, Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

Gwamnan Babban Banki CBN Ya Dawo Najeriya, Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

  • Gwamnan babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya koma bakin aiki bayan hutun karshen shekara da ya tafi waje
  • A wata sanarwa da CBN ya fitar dauke da sa hannun Daraktan hulda da jama'a, ya ce gwamnan ya koma Ofis yau Litinin
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ta kace-nace a sassan Najeriya kan zargin cin hanci da kuma alaka da ta'addanci

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa gwamnan bankin da ake ta cece kuce a kansa, Godwin Emefiele, ya dawo bakin aiki bayan hutun da ya tafi kasar waje.

Babban bankin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Daraktan sashin hulda da jama'a na CBN, Osita Nwanisobi, ya fitar ranar Litinin (yau).

Godwin Emefiele.
Gwamnan Babban Banki CBN Ya Dawo Najeriya, Ya Kama Aiki Gadan-Gadan Hoto: punchng
Asali: Depositphotos

Babban Bankin yace Godwin Emefiele, ya koma bakin aiki ne yau 16 ga watan Janairu, 2023.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: DSS ta yi karin haske game batun mamaye ofishin gwamnan CBN

Sanarwan da CBN ya wallafa a shafinsa na Tuwita ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele,ya koma Ofis don ci gaba da aiki bayan hutun shekara da ya tafi kasar waje."
"Mista Godwin Emefiele, wanda ya ɗauki hutun a watan Disamban shekarar da ta gabata ya koma bakin aiki ne yau Litinin 16 ga watan Janairu, 2023."
"Gwamnan ya dawo aiki da karsashin sauke nauyin da ke kansa yayin da ake shirin gudanar da taron kwamitin tsarin takardun kudi na farko da aka tsara yi ranar 23 ga watan Janairu, 2023."

Sanarwan ta kara da cewa Emefiele, a shirye yake ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata kamar yadda ya yi alkawarin yi gabanin shiga Ofis.

"A ko da yaushe Mista Emefiele a shirye yake ya aiwatar da aikin dake gabansa bisa rantsuwar kama aikin da ya yi da kuma tsarin umarnin shugaban kasa, Muhammadu Buhari."

Kara karanta wannan

Rudani: Ta karewa gwamnan CBN yayin da jami'an DSS ta mamaye ofishinsa da yamma

"Yayin da muke gode wa mutane bisa yarda da banki, muna rokon 'yan Najeriya su ci gaba da goyon bayan tsarukan babban banki masu nufin saita tsarin kudi da fargaɗo da tattalin arziki."

Majalisa ta ja da tsarin CBN

A wani labarin kuma A 2022 majalisar wakilan tarayya ta gayyaci gwamnan CBN domin ya musu karin haske kan wasu batutuwa da suka shige duhu

Sai dai har sau biyu mambobin majalisar ta zuba ido su ga kafafun Emefiele amma sai dai su ga isowar wasikar uzuri daga CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel