Katsina: Dakarun Soji Sun Halaka Gogarman 'Dan Bindiga, Kachalla, a Katsina

Katsina: Dakarun Soji Sun Halaka Gogarman 'Dan Bindiga, Kachalla, a Katsina

  • Ba a ritsa kwanaki 4 bayan shugaba Buhari ya ba 'yan Najeriya tabbacin tsaro ba, dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar sheke 'yan ta'adda da dama duk da Ibrahim Kachalla Gudau
  • An bakado yadda Gudau ya jagoranci harin da 'yan bindiga suka kaiwa jami'an tsaro farar hula yayin da suke kan aiki gami da halaka 7 a Kaduna makon da ya gabata
  • Sai dai, hoton gawar hatsabibin tayi yawo a yanar gizo, wanda yake daya daga cikin wadanda dakarun suka sheke yayin dakile harin kauyen Kankami ranar Lahadi a jihar Kaduna

Katsina - Kasa da kwanaki hudu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba 'yan Najeriya tabbacin mulkinsa zai tabbatar da samar da tsaro, dakarun rundunar sojin Najeriya sun bindige 'yan bindiga da dama, har da Ibrahim Kachalla Gudau.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Miyagu Sun Kai Farmaki Coci a Katsina, Sun Yi Garkuwa da Mutum 25

Taswirar Katsina
Katsina: Dakarun Soji Sun Halaka Gogarman 'Dan Bindiga, Kachalla, a Katsina. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Gudau, wani gawurtaccen 'dan ta'adda sannan daya daga cikin shugabannin 'yan ta'adda masu hatsarin gaske, ya na jagorantar tawagar hatsabiban da ke garkuwa gami da halaka mutane a yankunan Kaduna, Katsina, Zamfara da yankin jamhuriyar Nijar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi imani, tawagar Gudau ta halaka jami'an tsaro bakwai na tsaron farar hula (NSCDC), wadanda 'yan bindiga sukawa kwantan bauna gami da halakasu a jihar Kaduna yayin da suke kan aiki a makon da ya gaba.

Kamar yadda binciken sirrin da aka samu ya bayyana, Gudau, wanda hoton gawarsa yayi yawo a yanar gizo, ya na daya daga cikin wadanda dakarun suka sheke yayin da suka dakile wani gagarumin hari a kauyen Kankami na jihar Kaduna.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito yadda Buhari a makon da ya gabata yayi alkawari ga 'yan kasa kan tabbatar da tsaro gami da mayar da hankali wajen bunkasa tattalin arziki, kafin mika mulki da ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Halaka Basarake a Jihar Arewa, Gwamna Ya Kakaba Dokar Zaman Gida

Shugaban kasar ya fadi hakan ne yayin da ya tarbi taron mambobin cocin Katolika na Najeriya (CBCN) a gidan gwamnati da ke Abuja, ranar Laraba.

'Yan bindiga sun kai farmaki cocin Katsina, sun sace masu bauta

A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga sun kai hari wata majami'a da ke Jan Tsauni a Kankara da ke jihar Katsina.

An gano yadda suka tasa keyar mutum 25 tare da barin fasto cikin miyagun raunika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel