An Kama Daya Daga Cikin Wadanda Suka Sace Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya

An Kama Daya Daga Cikin Wadanda Suka Sace Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya

  • Gwamnatin jihar Edo ta bayyana cewa daukar matakin gaggawa da jami'an tsaro suka yi ya fara haifar da da mai ido
  • A ranar Asabar da yamma ne wasu mahara suka yi awon gaba da Fasinjoji a tashar jirgin kasa ta Edo
  • Yan sanda sun sanar da cewa sun yi nasarar kubutar da mutane 5 daga cikin wadan da lamarin ya shafa

Edo - Gwamnatin jihar Edo, ranar Lahadi, ta sanar da cewa an kama wani mutum daya da ake zargin yana da hannu a sace Fasinjojin Jirgin kasa a tashar Igueben ranar Asabar.

Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa akalla Fasinja 30 yan bindiga suka sace wadanda ke jiran Jirgin kasa a tashar dake karamar hukumar Igueben da misalin karfe 4:00 na yamma.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hukumar NRC Ta Rufe Tashar Jirgin Kasa da Yan Bindiga Suka Kai Hari

Harin jirgin kasa.
An Kama Daya Daga Cikin Wadanda Suka Sace Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya Hoto: tribune
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai kan lamarin, kwamishinan sadarwa da wayar da kai na Edo, Chris Osa Nehikhre, ya bayyana harin da abu mai walaha da gwamnati ta taba gamuwa da shi.

Nehikhre ya kara da cewa nan take bayan faruwar lamarin yan sanda da sauran jami'an tsaro suka bazama dazuka da nufin ceto Fasinjojin da kama maharan, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa Kokarin da ake ya fara haifar da sakamako mai kyau domin an kama mutum daya ada ake zargin dan tawagar masu garkuwan ne kuma ya fara bayani.

"Ba tantama jiya ta zo mana da wahala tun bayan shigowar sabuwar shekara, wasu yan bindiga sun sace Fasinjoji 32 a tashar jirgin kasa ta Igueben. Mataimakin gwamna, Philip Shaibu, ya ziyarci wurin."
"Labari mai dadi da ya iso wa gwamnati shi ne daya daga cikin maharan ya shiga hannu kuma ya fara bayanin da zai taimaka wa jami'an tsaro su shawo kan lamarin."

Kara karanta wannan

An Kuma Sace Fasijojin Jirgin Kasan A Nigeria Shekara Guda Bayan Sace Fasijojin Jirgin Abuja Zuwa Kaduna

"Gwamnati karkashin gwamna Godwin Obaseki na mika jinjina ga 'yan sanda, 'yan Bijilanti wadanda suka bazama, da ma Mafarautan yankin bisa kokarin da suke na ceto fasinjojin."

Jami'an tsaro sun ceto mutum 5

Daily Trust tace zuwa yanzun rundunar 'yan sanda ta yi nasarar ceto mutane 5 da lamarin ya rutsa da su ciki har da wani jami'in dan sanda da ya yi Ritaya.

Rahoto ya nuna cewa gamayyar jami'an tsaro da suka bazama cikin jejin ne suka samu nasarar kubutar da mutanen cikin koshin lafiya.

Kakakin rundunar yan sandan Edo, Chidi Nwanbuzor, wannan nasara ta samu ne da taimakon sauran hukumomin tsaro hadi da yan Bijilanti da Mafarauta.

Yace:

"Duk da har yanzu bamu tabbatar da yawan fasinjojin da aka sace ba amma mun fara samun nasarori. Daga cikin waɗanda jami'ai suka ceto har da dan sanda mai ritaya, wata da jaririnta dan shekara daya da kuma yara mace da namiji."

Kara karanta wannan

Manyan Dalilai Uku da Zasu Ja Hankalin 'Yan Arewa Su Zabi APC a 2023, Gwamna

"Yan sanda da sauran hukumomin tsaro; Dakaraun Edo, yan bijilanti da mafaraunta suna ci gaba da tsefe dajin don ceto Fasinjojin cikin koshin lafiya da kama yan ta'addan."

A wani labarin kuma gwamnatin tarayya ta rufe tashar jirgin kasa da yan ta'adɗa suka kai hari a jihar Edo

Hukumar NRC mai kula da harkokin sufurin jiragen kasa a Najeriya ta sanar da rufe tashar Ekehen ta jihar Edo bayan abinda ya faru.

Hakan ya biyo bayan harin da yan bindiga suka kai tashar, suka sace Fasinjoji da yawa, wasu da dama na kwance a Asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel