Hukumur Sufurin Jiragen Sama Ta Dakatar da Jirgin Kasa Na Jihar Edo

Hukumur Sufurin Jiragen Sama Ta Dakatar da Jirgin Kasa Na Jihar Edo

  • Hukumar NRC ta kasa ta sanar da cewa ta rufe tsahar jirgin kasa da yan bindiga suka kai hari da yammacin jiya Asabar
  • A wata gajeruwar sanarwa da NRC ta fitar ranar Lahadin nan, tace tashar zata ci gaba da zama a kulle har sai baba ta gani
  • A ranar Asabar ne wasu yan bindiga suka farmaki fasinjojin da ke jiran jirgi, sun yi won gaba da mutane masu yawa, sun jikkata wasu

Ondo - Hukumar sufurin jiragen kasa (NRC), ranar Lahadi ta sanar da rufe tashar Jirgin kasa ta jihar Edo har sai baba ta gani.

Jaridar Puch ta ruwaito cewa hukumar ta ce wannan matakin ya zama tilas biyo bayan tabarbarewar matsalar tsaro da harin da yan bindiga suka kai tashar.

Jirgin kasa.
Hukumur Sufurin Jiragen Sama Ta Dakatar da Jirgin Kasa Na Jihar Edo Hoto: punchng
Asali: UGC

Lamarin dai ya auku ne kusan shekara dayan bayan harin 28 ga watan Maris, 2020, wanda 'yan ta'adda suka kaiwa Jirgin kasan Kaduna-Abuja, kusan Fasinjoji 14 suka mutu, aka sace 65.

Kara karanta wannan

2023: Ana Zaman Jiran Zabin G5, Atiku da PDP Sun Yi Babban Kamu a Jihar da APC Ke Mulki

A sanarwan da NRC ta saki a dandalin whatsapp wanda yan jarida suka samu, tace an rushe tashar ne har sai baba ta gani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ruwayar Vanguard, Sanarwan tace:

"Muna mai sanarwa daukacin al'umma musamman Fasinjojin mu cewa mun rufe tashar Ekehen na ɗan lokaci saboda abubuwan da suka shafi tsaro, har sai lokacin da aka ji sanarwa daga gare mu."
"Sakamakon abinda ya faru a tashar Ekehen ranar Asabar, jirgin kasa ba xai sake tsayawa a tashar ba. Dan Allah kwastomomin mu su san wannan."

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun faramki Fasinjojin dake jiran jirgin kasa daga tashar Igueben, karamar hukumar Igueben ranar Asabar da yamma.

Maharan sun yi awon gaba da Fasinjoji masu yawa yayin da wasu da dama suka jikkata. Kakakin rundunar yan sandan Edo, Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Shugaban Majalisar Dokoki a Jihar Arewa

Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Sace Kakakin Majalisar Dokokin Filato

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Shugaban Majalisar Dokoki a Jihar Filato

An ce maharan dauke da makamai sun biyo sawun kakakin Majalisar da misalin karfe 11:30 na dare a wata motar Honda CR-V har zuwa gidansa da ke Low-Cost, Jos.

Amma jajircewar yan sanda masu gadin gidansa da kuma dauki kan lokaci ne ya sa jami'an tsaro suka yi nasarar dakile tuggun yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel