Yan Bindiga Sun Sace Mutane Da Dama A Tashar Jirgin Kasa

Yan Bindiga Sun Sace Mutane Da Dama A Tashar Jirgin Kasa

  • Shekara guda bayan sace, kashe tare da jikkata fasinjojin jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna a Nigeria an sake kwatawa
  • Sakamakon Lalacewar hanyoyi da wasu matsaltsalu na kunji-kunji mutane da dama ke gujewa amfani da hanoyin titin inda suke canjawa zuwa jirgin kasa ko na sama
  • Wannan sace mutane ba irin wancan bane, domin wannan a tashar akai satar da kuma wasu abubuwa da suka fariu

Edo - Yan bindiga sun kai hari a tashar jirgin kasa dake karamar hukumar Igueba a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Nigeria tare da yin garkuwa da gwamman fasinjoji. Rahotan BBC Hausa

Rohotannin da suke zuwa sun ce lamarin ya faru ne a dai-dai lokacin da fasinjojin jirgin ke shirin hawa jirgin wanda zai tashi da garin zuwa Warri dake jihar Delta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hukumar NRC Ta Rufe Tashar Jirgin Kasa da Yan Bindiga Suka Kai Hari

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da rundunar yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzr yace har zuwa yanzu da ake hada wannan rahotan ba'a samu labarin wani ya rasa ransa ba sai dai akwai jikkata.

Jirgi
Yan Bindiga Sun Sace Mutane Da Dama A Tashar Jirgin Kasa Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace lamarin ya faru ne kamar haka:

"Yan bindiga ne dauke da bindigogi da makamai suka far wa tashar jirgin kasan da maraicin ranar Asabar in da suka rika harbi baji ba gani kan mai uwa da wabi, sannan suka kama wasu fasinjojin da suke tashar".

Jaridar Thisday ta rawaito cewa yan Bindigar dauke da bindiga kirar AK47, sun fara harbi a sama kafin kuma sun budewa mutane wuta.

Jaridar ta kara da cewa lmarin ya faru ne da misalin karfe 4 da doriya na yamma. Wasu daga cikin fasinjojin sun bazama cikin daji wanda har yanzu ba'a san inda suka ba.

Kara karanta wannan

‘Yan Ta’adda Sun Kuma Kai Mugun Hari, Sun Dauke Mutane da-dama a Tashar Jirgin Kasa

Hari Makamancin wannan Da Zai Zauna A Zukatan Yan Nigeria

Wannan dai batun na zuwa ne kasa da shekara guda bayan da yan bindiga da suke da alaka da mayakan Al-anssar da suke Kaduna sukai harin kan Jirgin da yake tasowa daga Abuja zuwa Kaduna.

Faruwar Lamarin sai da ya tilastawa mahuktan Nigeria dakatar da zirga-zirgar jigin kusan na watanni 8, saia a watan Disamban nan aka dawo dashi da kuma wasu sharudan hawa jirgin tare da karfafa tsaro a hanayar da tashohin jirgin

Asali: Legit.ng

Online view pixel