Dalilan da Suka Sa Mazauna Filato da Sauran Jihohi Zasu Zabi APC, Lalong

Dalilan da Suka Sa Mazauna Filato da Sauran Jihohi Zasu Zabi APC, Lalong

  • Gwamnan Filato yace abu uku, samar da zaman lafiya, ci gaba da kamanta adalci zasu sa mutanen Filato su sake zaben APC
  • Simon Lalong, darakta janar da PCC-APC, yace ba Filato kadai ba, sauran jihohin Najeriya ba zasu watsar da APC ba
  • Ya gode wa daukacin mutanen jihar Filato bisa goyon bayan da suka ba gwamnatinsa kana ya bukaci ganin hakan a ranar zabe

Plateau - Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya bayyana yakininsa cewa mazauna jihar, jihohin arewa da sauran jihohin Najeriya zasu dangwala wa APC a babban zabe mai zuwa.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa yayin da gwamnan ke bayyana dalilansa, yace 'yan Najeriya baki daya zasu zabi APC ne saboda nasarorin da ta samu a bangaren zaman lafiya, ci gaba da kamanta adalci.

Kara karanta wannan

Ka yi hakuri, ba zan ba da ba: Gwamnan PDP a Arewa ya hana Buhari filin kamfen

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong.
Dalilan da Suka Sa Mazauna Filato da Sauran Jihohi Zasu Zabi APC, Lalong Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Lalong, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a inuwar APC ya fadi haka ne a wurin bikin Al'ada Bit Pol da aka shirya domin murnar sabuwar shekara a mahaifarsa, N’yak, karamar hukumar Shendam.

Gwamnan Filato a mulkinsa jam'iyyar APC ta yi manyan abubuwa domin dawo da zaman lafiya a jihar Filato, ta kuma magance cin zali, wariya da kuma rabuwar kai tsakanin al'umma.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa hakan ta faru ne bayan gwamnatinsa ta sake sabunta masarautun gargajiya da kuma kirkiro wasu sabbi domin kowa ya san ana tafiya da shi a harkokin jiha.

Haka zalika a ruwayar Guardian, gwamnan yace gwamnatinsa ta kirkiro hukumar gina zaman lafiya kuma ta ware fagen tattaunawar samun maslaha, fahimta da kuma hada kai.

Daga nan ya mika godiya ga mutanen jihar bisa goyon bayan da suka ba shi da kuma zaben APC. Bisa haka yana fatan wannan goyon baya zai fito baro-baro ranar zabe idan suka zabi Tinubu ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

2023: Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Bayanai Masu Muhimmanci Kan Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Sha Kaye

Haka nan Lalong ya bukaci mutane su ci gaba da ba su goyon baya ta hanyar zaben Dakta Nentawe Yilwatda, dan takarar gwamnan Filato a inuwar APC.

Dikko Radda ya karbi masu sauya sheka daga PDP

A wani labarin kuma Dan Takarar Gwamnan Ya Takaita Atiku, Jiga-Jigai da Mambobin PDP Sun Koma Bayan Tinubu

Dan takarar gwamnan Katsina na APC, Dikko Radda, ya karbi daruruwam masu sauya sheka daga PDP a kananan hukumomi biyu.

Dakta Radda yayi alkawarin samar da ayyukan yi ga matasa, dawo da zaman lafiya, inganta lafiya da habaka Noma idan aka zabe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel