Yan Bindiga Sun Kai Faramaki Gidan Wani Sarki A Kaduna, Sun Sace Ma'aurata

Yan Bindiga Sun Kai Faramaki Gidan Wani Sarki A Kaduna, Sun Sace Ma'aurata

  • Yan bindiga sun kai hari gidan marigayi tsohon Sarkin Jere, karamar hukumar Kagarko, sun yi awon gaba da mata da miji
  • Bayanai sun nuna cewa matar ta samu nasarar kubuta daga hannun yan ta'adda yayin da suka sake shiga gidan makota
  • Har yanzu babu sanarwa a hukumance daga hukumomi a jihar Kaduna amma majiyoyi da dama sun tabbatar

Kaduna - 'Yan bindigan daji sun kai hari gidan Marigayi Sarkin Jere, karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna, Marigayi Dakta Sa'ad Usman.

Jaridar Daily Trust tace maharan sun yi awon gaba da wani bawan Allah mai suna, Hussaini da matarsa da kuma ɗan jaririnta dan kimanin watanni hudu.

Yan fashin jeji.
Yan Bindiga Sun Kai Faramaki Gidan Wani Sarki A Kaduna, Sun Sace Ma'aurata Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Wani mazaunin Garin Jere, Mua'zu Adamu, wanda ya tabbatarwa yan jarida da faruwar harin ta wayar tarho, yace lamarin ya auku ranar Lahadi da karfe 11:23 na dare.

Kara karanta wannan

An Samu Babbar Matsala: Wasu Jiragen Sama Sun Yi Karo a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta

Ya ce matar ta samu nasarar tserewa daga hannun maharan yayin da suka yi yunkurin sake shiga wani gida a Anguwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adamu ya bayyana cewa yan bindigan, wadanda suka zo da mayaka da yawa dauke da makamai, sun zarce Anguwar Salanke suka sace mutum daya, Baba Na'ibi, kana suka jikkata wasu biyu.

Yace:

"A gaskiya, harsashi ya samu wani mutum daya sa'ilin da 'yan bindiga suka harbi Tagar gidan Baba Na'ibi yayin da na biyu ya ji rauni daga ƙarfen tagar da ta farfashe."

Ya kara da cewa tuni aka garzaya da mutanen biyu zuwa Asibiti domin a masu magani.

Masarautar Jere ta tabbatar da kai harin

Sakataren Masarautar Jere, Malam Aliyu Zubair, ya tabbatar da lamarin garkuwa da mutanen inda yace mutane shida maharan suka yi awon gaba da su a iya bayanan da ya tattara.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Harin Bam Kan Ayarin Wani Tsohon Gwamna

Ya ce 'yan fashin dajin sun mamayi gidan marigayi Sarkin ne da karfe 10:12 na daren ranar Lahadi daga bisani suka shiga gidan makota suka dauki mutane 5.

"Kuma kafin zuwan yan sanda maharan sun kama gabansu, 'yan banga ne suka yi kokarin fafatawa da su amma suka ci karfinsu saboda sun fi su manyan makamai."

Har yanzun babu sanarwa a hukumance daga rundunar yan sandan Kaduna kan wannan sabon harin.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Harin Bam Kan Ayarin Wani Tsohon Gwamna a Jihar Imo

Bayanai sun nuna cewa harin wanda aka kulla da nufin tsohon gwamnan ya yi ajalin jami'an 'yan sanda hudu da ke ba shi tsaro.

Tun daga Owerri, babban birnin.jihar Imo aka turo karin jami'an tsaro suka raka jigon siyasar har gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel