Jirgaen Helikwafta Biyu Sun Yi Taho Mu Gama da Sararin Sama, Mutane Sun Mutu

Jirgaen Helikwafta Biyu Sun Yi Taho Mu Gama da Sararin Sama, Mutane Sun Mutu

  • Jiragen Helikwafta biyu sun yi karo da juna a sararin samaniya a kasar Australia ranar Litinin da ta gabata, mutum hudu sun mutu
  • Hukumomi a kasar sun tabbatar da faruwar lamarin kuma a cewar 'yan sanda wasu mutane uku na kwance a Asbiti rai hannun Allah
  • Ma'aikatar Sufurin kasar ta ce tuni ta kaddamar da bincike kan lamarin domin gano abinda ya haddasa haduwar jiragen

Wasu Jiragen sama masu saukar Angulu sun yi karo da juna a sararin sama kuma akalla mutane hudu ne suka rasa rayuwarsu ranar Litini a wurin bude ido na ƙasar Australia.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa mahukunta sun tabbatar da aukuwar hatsarin tare da wallafa Hoton wurin wanda ya nuna fiffiken wani jirgin a kan tulin Yashi.

Hadarin jirgi.
Jirgaen Helikwafta Biyu Sun Yi Taho Mu Gama da Sararin Sama, Mutane Sun Mutu Hoto: vanguardngr.
Asali: UGC

Hukumar 'yan sandan kasar ta bayyana cewa ba ya ga wadan da suka mutu a hadarin, wasu mutum uku na kwance rai hannun Allah a Asibiti.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Harin Bam Kan Ayarin Wani Tsohon Gwamna

Daya daga cikin jiragen biyu ya tuntsure kasa yayin da Fukafukinsa ya yi gefe guda a kan yashi kusa da gabar babban Teku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika a Hoton da aka wallafa ya nuna cewa ɗayan jirgin ya sauka dai-dai a wurin hatsarin kuma babu abinda ya fita daga jikinsa.

Tuni wani Jirgin na daban ya kawo ɗauki wurin yayin da jami'an ba da Agaji suka mamaye wurin don ceto waɗan da hatsarin ya rusta da su.

Mukaddashin Sufetan 'yan sanda na Queensland, Gary Worrell, ya fada wa manena labarai cewa:

"Bayan jiragen biyu suka ci karo a sama, sun rikito ƙasa, suka sauka a kan Yashi kusa da Tekun World resort. Sakamakon haka mutane hudu suka rasa rayukansu, wasu uku na kwance a Asibiti cikin mawuyacin hali."

Tuni dai ma'aikatar Sufuri ta kasar Australia ta kaddamar da bincike don gano abinda ya haddasa hatsarin wanda ta kira da, "Karon sama."

Kara karanta wannan

Babu Nakasasshe Sai Rage: Bidiyon Mai Nakasa Yana Kasuwanci A 'Yar Kekensa

Jirgin Rundunar Sojin Kasar Nijar Ya Yi Hatsari

A wani labarin kumaJirgin Helikwafta na rundunar sojin sama a kasar Nijar ya yi hatsari yayin da yake kokarin sauka a filin jirgin Niamey

Ma'aikatar tsaron ta ce haɗarin ya faru ne lokacin da jirgin Helikwaftan kirar ƙasar Rasha Mi-17 chopper ya dawo daga shawagin ɗaukar horo.

Kasar Nijar mai makoftaka da Najeriya na fama da matsalolin ta'addancin 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel