Hadimin Gwamnan Jihar Ebonyi Ya Mutu a Wani Mummunan Hatsari

Hadimin Gwamnan Jihar Ebonyi Ya Mutu a Wani Mummunan Hatsari

  • Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya rasa ɗaya daga cikin hadimansa sanadin hatsarin motan da ya rutsa da shi ranar Lahadi
  • Rahotanni sun bayyana cewa Mista Sunday Agwu ya rasu ne ranar Litinin da safe a wani Asibiti da ba'a faɗi sunansa ba
  • Idan baku manta ba a makon da ya shige wasu miyagu suka harbe wani hadimin gwamnan jihar Ebonyi

Ebonyi - Wani hadimin gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, Mista Sunday Agwu, ya rasa rayuwarsa sanadiyyar hatsarin mota da ya rutsa da shi jiya Lahadi.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa shagalin murnar kirsimetin iyalansa ya sauya zuwa jimami bisa la'akari da matsayinsa da nauyin da yake ɗauka a gidan.

Sunday Agwu.
Hadimin Gwamnan Jihar EbonYi Ya Mutu a Wani Mummunan Hatsari Hoto: vanguard
Asali: UGC

Mista Agwu, kodinetan cibiyar cigaba ta ƙaramar hukumar Ishielu a jihar Ebonyi, ya rasa rayuwarsa ne a kan hanya saboda gudun tsiya a Titi a wata ruwayar kuma an ce an y yunkurin yin asiri ne da shi.

Kara karanta wannan

Dan Sanda Ya Harbe Wata Lauya a Hanyarta Ta Dawowa Daga Coci a Ranar Kirsimeti

Rahotanni sun bayyana cewa ya rasu ne da safiyar Litinin ɗinnan a Asibiti da ba'a bayyana ba kuma tuni aka mayar da gawarsa ɗakin ajiye gawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya da ba a tabbatar da ingancin ta ba ta yi ikirarin cewa marigayin ya gamu da ajalinsa ne a Motarsa a kan babban Titin Enugu-Abakaliki.

Shugaban karamar hukuma ya yi ta'aziyya

Da yake martani kan lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Ishielu, Obinna Onwe, ya ayyana mutawar Agwu a matsayin wani babban rashi da zai wuya a maye gurbinsa a yankin.

Ya kuma bukaci iyalan mamacin da su miƙa al'amarin su ga Allah domin shi kaɗai yasan dalili da kuma laokacim mutuwar kowa, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa idan baku manta ba a makon da ya gabata, wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne suka harbe wani hadimin gwamnan Ebonyi a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

"Abin Da Ya Janyo Rasuwar Ƴaƴa Na 2", Buhari Ya Yi Magana Kan Wani Sirrinsa Mai Sosa Zuciya

Hadimin, mamba a hukumar majalisar dokokin jihar Ebonyi, Barista Leonard Chibuzor Alegu, ya rasu ne sakamakon harbinsa da wasu 'yan bindiga suka yi.

A wani labarin kuma Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP a Jihar Oyo Ya Rasu Yana Da Shekaru 62 a duniya

Rahotanni sun nuna cewa ya rasu ne ranar Laraba, 21 ga watan Disamba, 2022 a Asibitin jami'ar jiha da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kudu maso yammacin Najeriya.

Marigayi Olayiwola, ya rike kujerar Sakataren jam'iyyar PDP ne a zamanin mulkin marigayi tsohon gwamnan Oyo, Adebayo Alao-Akala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel