"Abin Da Ya Janyo Rasuwar Ƴaƴa Na 2", Buhari Ya Yi Magana Kan Wani Sirrinsa Mai Sosa Zuciya

"Abin Da Ya Janyo Rasuwar Ƴaƴa Na 2", Buhari Ya Yi Magana Kan Wani Sirrinsa Mai Sosa Zuciya

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya rasa yayansa biyu da suka haifa da matarsa na farko, Safinatu, saboda ciwon sikila
  • Shugaban kasar ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 23 ga watan Disamba, lokacin liyafar cin abinci da aka shirya don murnar cikarsa shekara 80 da haihuwa
  • Hakan yasa kafin Buhari ya auri first Lady, Aisha, sai ya da tabbatar jininta AA ne don gudun rasa wasu yayansa

FCT Abuba - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a, 23 ga watan Disamba, a karon farko ya bayyana wa yan Najeriya cewa ciwon sikila ne yayi sanadin rasuwar yayansa biyu, Daily trust ta rahoto.

Buhari ya bayyana wannan abin mai sosa zuciya a wani bidiyo da aka nuna yayin liyafar cin abinci na musamman da iyalansa da aminansa suka shirya don murnar cikarsa shekaru 80, a ranar Juma'a 23 ga watan Disamba a Banquet Hall a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Abun da Yasa Ba Zan Yi Kewar Fadar Shugaban Kasa Ba, Buhari Ya Magantu

Buhari da Osinbajo
"Abin Da Ya Janyo Rasuwar Yaya Na 2", Buhari Ya Yi Magana Kan Wani Sirrinsa Mai Sosa Zuciya. Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban kasar ya kara da cewa Safinatu, tsohuwar matarsa da ta rasu ce mahaifiyar yayan da suka rasu.

An tattaro cewa wannan shine dalilin da yasa lokacin da zai auri first lady, Aisha Buhari, ya dage cewa dole matar da zai sake aure ya zama jininta AA ne, don kada yaransa su gaji S daga jininsa na AS.

Wacece Safinatu Buhari?

Safinatu malamar makaranta a Najeriya kuma first lady na Najeriya daga 1983 zuwa 1985. Ita ce matar Shugaba Muhammadu Buhari ta farko.

Ta hadu da Buhari lokacin tana da shekaru 14 kuma sun yi aure a 1971 lokacin tana da shekaru 18.

Sun haifi yaya 5 masu suna kamar haka; Zulaihatu (marigayiya), Magajiya-Fatima, Hadizatu-Nana, Safinatu Lami da Musa (marigayi).

Jibril daga Sudan: Buhari ya yi magana kan jita-jitar mutuwarsa

Kara karanta wannan

A Karshe Buhari Ya Fayyace Gaskiya Game Da Batun Karin Aurensa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magana kan jita-jitar da aka rika yadawa na cewa ya mutu kuma an maye gurbinsa da wani Jibril daga Sudan.

Shugaban na Najeriya ya ce abin bai masa dadi ba. Ya ce yana yi wa kallon abin ne a matsayin makirci da aka kirkira don kawar da hankalin yan Najeriya daga ayyuka gine-ginen raya kasa da cigaba da gwamnatinsa ke yi.

Ba gaskiya bane, ban taba yunkurin kara mata ba, In Ji Buhari

A bangare guda, Farfesa Yemi Osinbajo mataimakin shugaban kasa ya bayyana abin da Shugaba Buhari ya ce game da rade-radin cewa zai kara aure.

Osinbajo ya bayyana cewa Buhari ya fada masa cewa ba gaskiya bane, jita-jita ne kawai da zargi na mutane masu wata manufa nasu na daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel