Dan Sanda Ya Bindige Wata Lauya Har Lahira a Ranar Kirsimeti

Dan Sanda Ya Bindige Wata Lauya Har Lahira a Ranar Kirsimeti

  • Wani jami’in dan sanda ya katse rayuwar wata matashiya yar Najeriya a jihar Lagas bayan ya harbe ta kirjinta
  • Wacce abun ya ritsa da ita, Omobolanle Raheem, na a hanyarta ta dawowa daga coci a ranar Kirsimeti tare da mijinta lokacin da mummunan al’amarin ya afku
  • Rundunar yan sandan jihar Lagas ta tabbatar da kama dan sandan da ya yi kisan tare da abokan aikinsa biyu

Lagos - Wani jami'in dan sanda ya harbe wata lauya mai suna Misis Omobolanle Raheem, a yankin Ajah da ke jihar Lagas a ranar Kirsimeti.

Misis Omobolanle Raheem ta kasance mamba a kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) reshen jihar Lagas.

Lauyar da aka kashe da wani dan sanda
Dan Sanda Ya Bindige Wata Lauya Har Lahira a Ranar Kirsimeti Hoto: @InibeheEffiong
Asali: Twitter

Wani jami'i mai mukamin Mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) da ba a bayyana ba shine ya harbe ta.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa iyalan na a hanyarsu ta dawowa daga coci lokacin da mummunan al'amarin ya afku a karkashin gadar Ajah kuma kusa da wani ofishin yan sanda.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dan Bindiga a Kaduna, Sun Kwato Bindigogin AK47 Guda 4

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kama jami'in da ake zargi da kisan da wasu tawagarsa su biyu.

An yi zargin cewa jami'an yan sandan na karbar na goro a hannun masu ababen hawa a babban hanyan sannan suka bukaci mijin Raheem, wanda ke tuki ya faka motarsu.

A cewar abokin aikin marigayiyar, mijinta na rage gudu sannan yana jiran motar gabansu ya matsa don ya faka da kyau.

Ya ce:

"Wani jami'in dan sanda ya harbi uwar dakina Barista Omobolanle Raheem a hanyarsu ta dawowa daga coci ran Kirsimeti a karkashin gadar Ajah.
“Yanzun nan yan uwanta suka kirani cewa suna bukatar lauya da zai tsaya masu kafin yan sanda su sauya labarin.
"Sun dauki lamarin zuwa ofishin yan sanda na Ajiwe. Dan sandan ya fito ne daga ofishin Ajiwe.
"Mijinta ne ke tuka motar, Barista Omobolanle na zaune a kujerar gaba tare da mijinta.

Kara karanta wannan

An Kama Wani Mai Garkuwa Da Mutane Yana Karbar Kudin Fansa N3m Daga Iyayen Wanda Aka Sace A Jihar Arewa

"Jami'in dan sandan ya bukaci su faka kuma suna bukatar motar gabansu ta wuce don su iya fakawa, nan take dan sandan ya harbeta a kirjinta.
“Da ganin abin da ya faru, sai sauran yan sandan da ke bakin aiki sun tsere.
"Bayan dan wani lokaci, wasu yan sanda sun zo suka tafi da gawarta zuwa dakin ajiye gawa da ke Yaba, ba tare da izninin yan uwanta ba.
"Yanzu haka danginta sun gano inda aka kai gawarta.
"Yanzu haka bana Lagas. Na yi tunanin kawo maku nan ne don neman taimakonku."

Rundunar yan sanda ta yi martani

Kakakin yan sandan jihar Lagas, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa an tsare jami'in dan sandan da ya harbi lauyan tare da abokan aikinsa biyu da ke wajen da abun ya faru, Premium Times ta rahoto.

Ya ce an kwashi marigayiyar zuwa asibiti inda a nan ne ta mutu. Sai dai bai ambaci sunan jami'in dan sandan ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Kashe Basarake

Asali: Legit.ng

Online view pixel