Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP a Jihar Oyo Ya Rasu Yana Da Shekaru 62

Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP a Jihar Oyo Ya Rasu Yana Da Shekaru 62

  • Allah ya yi wa tsohon sakataren jam'iyar PDP mai mulki a jihar Oyo, Taofeek Olayiwola rasuwa yana da shekara 62 a duniya
  • Rahoto ya nuna cewa jigon siyasar ya riga mu gidan gaskiya ne a Asibitin jami'ar jiha da ke Ibadan babban birnin Oyo ranar Laraba 21 ga watan Disamba
  • Jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar PDP a jihar yace wanna babban rashi ne domin mamakin jigo ne kuma mara damuwa

Oyo State - Tsohon Sakataren Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Oyo, Taofeek Olayiwola, ya riga mu gidan gaskiya a Asibitin jami'a.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon Sakataren kuma jigo a jam'iyyar PDP ya rasu ne yana da shekaru 62 a duniya.

Taswirar jihar Oyo.
Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP a Jihar Oyo Ya Rasu Yana Da Shekaru 62 Hoto: punchng
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa ya rasu ne ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu, 2022 a Asibitin jami'ar jiha da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kudu maso yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ayarin Dakarun Yan Sanda Hari a Arewa, An Rasa Rayuka

Marigayi Olayiwola, ya rike kujerar Sakataren jam'iyyar PDP ne a zamanin mulkin marigayi tsohon gwamnan Oyo, Adebayo Alao-Akala.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai magana da yawun jam'iyyar PDP reshen jihar, Akeem Olatunji, shi ne ya tabbatar da wannan babban rashi ga manema labarai ta wayar salula.

Akeem Olatunji, ya ayyana marigayin da mutum mai saukin kai kuma babban ɗan siyasa jigo wanda ya yi imani da cewa akwai rayuwa kuma yake son a rayu.

Oyo na ɗaya daga cikin jiohin kudu dake hannun PDP sai dai gwamna mai ci, Seyi Makinde, wanda ke neman tazarce a zaben 2023, yana cikin masu neman Ayu ya yi murabus.

2023: Wani Babban Jigon PDP A Jihar Delta Ya Mutu A Hanyar Zuwa Taron Kamfe

A wani labarin kuma Jigon jam'iyyar PDP a jihar abokin gamin Atiku Abubakar watau Delta ya riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin ya rutsa da shi

Kara karanta wannan

Bude 'Border': Atiku ya fadi abin da zai yiwa iyakokin kasar nan idan ya gaji Buhari a 2023

Wasu bayanai da aka tattare sun ce Motarsa da yake ciki tare da maituƙa shi ne ta ci kato da babban Tankar dakon man fetur, nan take direban ya ce ga garin ku nan.

Marigayin ya kasancen ɗan ga ni kashe nin kakakin majalisat dokonin Delta, wanda a yanzu ke neman takarar gwamna a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel