An Shafa Fatiha, An Ɗaura Auren Ɗiyar Tsohon Gwamnan Zamfara da Ango Shema

An Shafa Fatiha, An Ɗaura Auren Ɗiyar Tsohon Gwamnan Zamfara da Ango Shema

  • Manyan jiga-jigan siyasa a Najeriya sun halarci wurin ɗaura auren diyar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdul'aziz Yari
  • Wasu Hotuna da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya wallafa a shafinsa ya nuna yadda aka ɗaura auren
  • Mataimakin shugaban kasa Farfesa, Yemi Osinbajo, gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato da wasu kusoshi a ƙasar nan sun halarta

Zamfara - An ɗaura auren ɗiyar tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma babban jigo a jam'iyyar APC, Abdul'aziz Yari, a ƙaramar hukumar Talatan Mafara dake jihar Zamfara.

Hadiza Abdul'aziz Yari ta Amarce da Angonta, Nasir Mamman Shema yau Asabar 24 ga watan Disamba, 2022.

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, da wasu jiga-jigan siyasa na APC da PDP sun halarci wurin ɗaura auren a Talatan Mafara, Zamfara.

Bukola Saraki ya wallafa Hotunan wurin ɗaura auren a shafinsa na dandalin sada zumunta watau Tuwita.

Kara karanta wannan

Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Rasuwa a Kano

Hotunan wurin daura aure

Wurin Daura aure.
An Shafa Fatiha, An Ɗaura Auren Ɗiyar Tsohon Gwamnan Zamfara da Ango Shema Hoto: @Bukolasaraki
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wurin daura aure.
An Shafa Fatiha, An Ɗaura Auren Ɗiyar Tsohon Gwamnan Zamfara da Ango Shema Hoto: @bukolasaraki
Asali: Twitter

Bukola Saraki.
An Shafa Fatiha, An Ɗaura Auren Ɗiyar Tsohon Gwamnan Zamfara da Ango Shema Hoto: @bukolasaraki
Asali: Twitter

Saraki ya wallafa a shafinsa cewa:

"Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, yanzu aka shafa fatiha aka ɗaura auren Hadiza Abdul'aziz Yari, ɗiyar tsohon gwamnan Zamfara, Alhaji Abdul'aziz Yari, da Angonta, Nasir Mamman Shema."

Daga cikin kusoshin siyasa a Najeriya da suka halarci wurin har da mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Yemi Osinbajo da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.

Ban zan taba rabuwa dashi ba, inji matar da ta auri wanda yafi kowa muni a duniya

A wani labarin kuma Matar da ta Auri mutumin da ake ganin yafi kowa muni a duniya tace tarayyarsu mutu ka raba

Kate Namanda itace mata ta biyu ga wanda yafi kowa muni a duniya kuma suna da 'ya'ya takwas tare wanda babban dan ke da shekara 20.

Kara karanta wannan

An Ɗaure Dattijo Dan Shekara 60 Watanni 6 a Yari Kan Sace Tabarmi da Wasu Kayayyaki

A wani hira da aka yi da ita da Afrimax English, Namanda ta bayyana cewa mutane sun zata ta haukace ne, amma daga baya duk sunyi nadamar abinda suka fada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel