An Daure Wani Dattijo Dan Shekara 60 Kan Ya Saci Tabarma Biyu

An Daure Wani Dattijo Dan Shekara 60 Kan Ya Saci Tabarma Biyu

  • Kotu ta ɗaure wani Dattijo watanni shida a gidan gyran hali bayan kama shi da laifin sata a makarantar da yake gadi
  • Mutumin ɗan shekara 60 a duniya mai suna Ɗanladi, an kama shi da laifin satar Tabarma da wasu kayayyaki
  • Daga baya Alkali ya ji tausyainsa ya rage masa hukuncin zaman Kurkuku zuwa watanni uku

Ondo - Wani Dattijo ɗan shekara 60, Pious Danladi, zai shafe watanni Shida a gidan gyaran hali sakamkon kama da shi laifin satar Tabarma da Kujeru a makarantar Apex Group of School dake Titin Ado Ekiti, Akure, jihar Ondo.

Jaridar The Nation ta rahoto cewan Ɗanladi yana aikin gadi ne a Makarantar kuma ya aikata wannan laifi ne na ɗan hannu a watan Disamba, 2021.

Gidan yari.
An Daure Wani Dattijo Dan Shekara 60 Kan Ya Saci Tabarma Biyu Hoto: thenation
Asali: UGC

Ba tare da bata lokaci ba, Ɗanladi ya amince da aikata laifin da ake tuhumarsa kwara ɗaya watau Sata.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Wa Matashi Ɗan Shekara 20 Ɗaurin Gidan Yari A Jihar Arewa Saboda Lalata Allunan Kamfen Ɗin Atiku

Mai shigar da ƙara na hukumar 'yan sanda, Insufekta Simon Wada, ya lissafa jerin kayayyakin da ake tuhumar mai gadin da sace wa da kuma darajarsu a kudin Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kayayyakin sun haɗa da, Kujerun Filastic 25 da ake ganin zasu kai N62,000, Bututun karfe na N50,000, Tabarmu guda biyu da suka kai N70,000, tukunyoyin girki na N35,000 da wasu kaya da zasu kai N189,000.

Dukkanin waɗannan kayayykin, wanda ake tuhuma ne ya sace su daga makarantar Apex Group of School, Akure, babbar birnin jihar Ondo ya je can a sayar.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya shaida wa Alkalin Kotun majirtire cewa Ɗanladi mai gadi ya sayar da waɗannan kayayyaki ga wasu mutane da ba'a san su ba.

Wane hukunci Kotu ta yanke?

Alkalin Kotun mai shari'a Damilola Sekoni, ya ce ya kama Ɗanladi da aikata laifin da ake tuhumarsa kuma ya yanke masa hukuman zaman Kurkuku na watanni Shida.

Kara karanta wannan

Dubbannin Malaman Makaranta a Arewa Sun Yunkuro, Sun Ayyana Wanda Zasu Goyi Baya a 2023

Daga baya Alkalin ya rage hukuncin Ɗaurin zuwa watanni uku domin ba Mai gadin dama ya yi aiki ya biya masu ƙara.

A wani labarin kuma Kotu Taki Amincewa Da Bukatar DSS Na Kama Gwaman Babban Bankin Najeriya (CBN)

Hukumar tsaro ta farin kaya ta nemi izinin Kotun ne domin kama gwamnan kan tuhume-tuhumen da suka haɗa da Zamba cikin aminci da sauransu

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ta cece-kuce kan sabon tsarin da CBN ya bullo da shi domin rage yawaitar yawon kudi a hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel