Ban zan taba rabuwa dashi ba, inji matar da ta auri wanda yafi kowa muni a duniya

Ban zan taba rabuwa dashi ba, inji matar da ta auri wanda yafi kowa muni a duniya

  • Matar Godfrey Baguma, wanda yafi kowa muni a duniya ta bayyana cewa mutanen da suka rika mata dariya a da yanzu sun dawo suna nadama
  • Kate Namanda itace mata ta biyu ga wanda yafi kowa muni a duniya kuma suna da 'ya'ya takwas tare wanda babban dan ke da shekara 20
  • Sunyi aure ne bayan sun haifi 'ya'ya hudu saboda rashin yarda daga iyalai da abokai

Matar Godfrey Baguma, wanda aka lakabawa da wanda yafi kowa muni a duniya ta bayyana cewa mutanen da suka rika mata dariya shekaru 28 da suka wuce yanzu sun dawo suna nadama hadi da ganin cewa a yanzu ya shahara.

Kate Namanda ta hadu da Godfrey Baguma ne ta hanyar dan uwanshi wanda shima yaje neman aure ne a yakin Kyazenga dake kasar Uganda.

Kara karanta wannan

Ta gudu ta barni: Dan acaba mai yawo da jariri a cikin riga ya fadi tarihinsa mai ban tausayi

A wani hira da aka yi da ita da Afrimax English, Namanda ta bayyana cewa mutane sun zata ta haukace ne, amma daga baya duk sunyi nadamar abinda suka fada.

Bamuga, matarshi da 'ya'yansu
Ban zan taba rabuwa dashi ba, inji matar da ta auri wanda yafi kowa muni a duniya
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya cika muni, bama kaunarsa," inji iyalin Namanda ga masoyin nata, amma Namanda wacce take kaunar masoyin nata abin bai taba damun ta ba kuma tayi alkawarin tafiya ta zauna da shi.

Haka ma ga kawayenta sun yi korafin cewa mutumin bai dace da kyawunta ba. Masoyan sai suka yi shawarar jinkirta aurensu saboda yadda duka iyalansu da masoyan nasu suka ki abin, suka yanke yin aure bayan da suka haifi 'ya'ya hudu.

A yanzu iyalai da abokansu suna nadamar abinda suka yi saboda yanzu Baguma da Namanda abin misali ne na ma'aurata wadanda suke cikin jin dadi kana da yanzu Baguma ya zamto duniya ta san dashi.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Kama Hayan Ɗaki 1, Ta Shirya Shi Tamkar 'Aljannar Duniya' Da Sabon Firinji, Talabijin Da Kayan Ɗaki

Da aka tambayeta ko ta aure shi ne dan kudinshi, Namanda tace, A da bashi dashi kuma hakazalika yanzu ma.

"Ba zan taba rabuwa dashi ba, kada ka damu," tace yayinda aka tambayeta idan da wani zai zo neman aurenta.

Ina Buƙatar Mijin Aure Cikin Gaggawa, In Ji Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya

A wani labarin, gogaggiyar jarumar fina-fina ta Nollywood a Najeriya wacce aka dade ana damawa da ita, Eucharia Anunobi, ta ce neman mijin aure ta ke yi cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

A wata tattaunawa da BBC Ibo ta yi da ita, ta ce tana neman namijin da zai sanya mata zoben aure a yatsan ta.

Jarumar mai shekaru 56 ta ce tana fatan samun cikakken namiji, wanda ya ke da duk abinda

Asali: Legit.ng

Online view pixel