Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Rasuwa a Kano

Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Rasuwa a Kano

  • Hanarabul Ghali Umar Na'abba ya yi rashin mahaifiyarsa, Hajiya Rabi, kuma an yi jana'izarta
  • An bizne Hajiya Rabi a jihar Kano bayan gudanar da Sallar Jana'iza da gomman mutane suka halarta
  • Mahalarta jana'izar sun yi addu'an Allah ya jikanta kuma ya gfarta mata kura-kuren da ta aikata

Kano - Allah ya yiwa Hajiya Rabi, mahaifiyar tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Ghali Umar Na'abba, rasuwa a jihar Kano.

Ghali Na'abba ya kasance Kakakin majalisar lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, tsakanin 1999 da 2003.

An gudanar da jana'izar mahaifiyar dan siyasan ranar Juma'a a Unguwar Gandun Albasa dake jihar Kano.

Jana'iza
Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Rasuwa a Kano Hoto: Aminu Dahiru
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jana'izar ya samu halartar Gwamnan jihar Kano, mataimakinsa da manyan jami'an gwamnatin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Dace A Sani Game Da Umar Namadi, Dan Takarar Gwamnan APC a Jigawa

Hadimin Ganduje, Aminu Dahiru, ya bayyana cewa Gwamnan ya yi addu'ar Allah ya rahamsheta kuma ya saka mata da gidan Aljannah.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar a shafin Gwamnan na Facebook, yace:

"Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR. tare da Mataimakin sa kuma dan Takarar Gwamna Dr. Nasiru Yusuf Gawuna sun halacci Janazar Hajiya Rabi, Mahaifiyar Hon. Ghali Umar Na'abba a Unguwar Gandun Albasa.
Mai Girma Gwamnan yayi addu'a akan Allah ya jikanta da rahma yasa Aljannah makomarta."

Allah ya yiwa shugaban kamfanin jirgin Max Air Rasuwa

Duk a yau Juma'a, labari ya yadu cewa Allah ya yiwa Alhaji Bishir Mangal, Shugaban Kamfanin Max Air, cikawa a birnin tarayya Abuja.

Alhaji Bishir ya kasance kani ga mammalakin kamfanin MaxAir kuma attajirin dan jihar Katsina, Alhaji Dahiru Barau Mangal.

Bayanai sun nuna cewa marigayin ya cika ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya da yayi.

Kara karanta wannan

Bago VS Kantigi: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan Yan Takara 2 a Jihar Neja

Hakazalika an gudanar da jana'izarsa misalin karfe biyar na yammacin Juma'a a cikin garin Abuja.

Jama'a sun yi addu'an Allah ya jikansa kuma ya gafarta masa kura-kuransa.

Mutuwa ranar Juma'a

Legit ta tuntubi Malamin addini kuma shugaban cibiyar Darul Irshad, Ustaz Abu Amir, inda ya bayyana falalar mutuwa ranar Juma'a.

A cewarsa:

"‘Abd-Allaah ibn ‘Amr ya ruwaito cewa: "Manzon Allah (SAW) ya ce: 'Babu Musulmin da zai mutu ranar Juma'a ko daren Juma'a face Allah ya kareshi daga jarabawar kabari."
Hadisi ne ingantacce da aka karbi daga al-Tirmidhi, 1074; kuma Albani ya ingantashi a Ahkaam al-Janaa’iz, p. 49, 50"

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel