PDP A Kano: Aminu Wali Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Bayan Kotu Ta Ba Wa Abacha Nasara

PDP A Kano: Aminu Wali Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Bayan Kotu Ta Ba Wa Abacha Nasara

  • Korarren dan takarar gwamnan PDP na jihar Kano a zaben 2023, Sadiq Aminu Wali ya ce bayyana cewa zai garzaya kotun daukaka kara bayan kotu ta yi watsi za zabensa
  • Wali yayin bayyanawa manema labarai rashin gamsuwarsa da hukuncin ya ce lauyoyinsa sun gano kura-kurai a kalla 20 a hukuncin da aka yanke na bawa Mohammed Abacha nasara
  • Jigon na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Katsina ya yi kira ga magoya bayansa da masoya da su kwantar da hankulansu yayin da lauyoyinsa ke cigaba da nazari kan hukuncin

Kano - Korarren dan takarar gwamna na PDP a jihar Kano, Sadiq Aminu Wali, ya bayyana niyarsa na zuwa kotun daukaka kara bayan babban kotun tarayya ta soke zabensa da aka yi a matsayin dan takarar gwamna a jihar.

Daily Trust ta rahoto cewa Babban Kotun Tarayya da ke Kano ta ayyana Mohammed Sani Abacha a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na PDP a Kano.

Kara karanta wannan

An Tsaida Ranar da Kwankwaso Zai Yi Jawabi a Chatham House, Zai Tallata Manufofinsa

Aminu Wali
PDP A Kano: Aminu Wali Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Bayan Kotu Ta Ba Wa Abacha Nasara. Hoto: Leadership
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin yanke hukuncin, Mai shari'a A.M. Liman ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sauya sunan Wali da na Abacha.

Daga nan kotun ta amince da zaben fidda gwani na bangaren Shehu Sagagi da aka gudanar a Lugard House, wacce ta samar da Abacha a matsayin dan takarar gwamna a maimakon na bangaren Wali da aka gudanar a cibiyar matasa na Sani Abacha.

Martanin Wali

Da ya ke magana da yan jarida a Kano, Wali ya yi kira ga magoya bayan PDP su kwantar da hankulansu, yana mai cewa lauyoyinsa na nazarin 'hukuncin mai dauke da kuskure' domin daukaka kara.

A cewarsa, lauyoyinsa tuni sun gano kura-kurai a hukuncin, wacce ta bashi kwarin gwiwa na kwato abin da ya kira 'ikon da Kanawa' a kotun daukaka kara.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara

Mun gano kura-kurai fiye da 20 a hukuncin koran Wali, Nasir Aliyu

A bangarensa, lauyan Wali, Nasir Adamu Aliyu (SAN) ya ce sun gano kura-kurai fiye da 20 don kare kansu a kotun daukaka kara, Daily Trust ta rahoto.

A cewar Aliyu, Wali ya yi nasara a kotun daukaka kara lokacin da Ja'afar Sani Bello ya shigar da kara yana kalubalantar zaben fidda gwani bayan an yi zabe bisa ka'ida kum jam'iyyar PDP ta kasa ta sa ido a kai.

Kotu Ta Fatataki Wali, Ta Tabbatar Da Mohammed Abacha A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A PDP

Tunda farko, kun ji cewa Kotun tarayya a jihar Kano, a ranar Alhamis, ta tabbatar da Mohammed Sani Abacha, a matsayin halastaccen zababben dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Kano.

Mai sharia AM Liman, yayin hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis ya soke zaben fidda gwani da ta samar da Sadik Aminu Wali.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Kori Wali, Ta Tabbatar Da Abacha A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A PDP

Hakazalika, kotun da bawa hukumar zabe mai zaman kanta INEC umurnin ta sauya sunan Wali da na Mohammed Sani Abacha a cewar rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel