Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara

Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara

  • Gwamnatin Najeriya ta ware ranakun Litinin 26 da Talata 27 don hutun bikin kirsimeti, boxing day
  • Har wa yau gwamnatin ta ware ranar 2 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar hutun sabon shekara
  • Gwamnati ta bukaci al'ummar kasar su yi amfani da bikin don yi wa kasa addu'ar samun zaman lafiya kuma su so juna

Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Litinin 26 da Talata 27 ga watan Disamban 2022 da 2 ga watan Janairun 2023 a matsayin hutu don bikin kirsimeti, Boxing day da sabuwar shekara kamar yadda aka jera.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya cikin sanarwa mai dauke da sa hannun M.L. Belgore, sakataren dindindin na ma'aikatan a ranar Alhamis.

Aregbesola
Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Yayin da ya ke taya kiristoci murnar kirsimeti da sabuwar shekara, Aregbesola ya yi kira gare su da suyi koyi da halayen Annabi Isa (AS) musamman imani, kauna da soyayya, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sabuwar kitimurmura: Ba mu san adadin sabbin Naira da aka buga ba, inji CBN

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Dole mu yi koyi da halayen Annabi Isa (AS) da koyarwarsa na kankan da kai, hidima, tausayi, hakuri, zaman lafiya, ga gaskiya da haihuwarsa koyarwa. Wannan shine hanya mafi dacewa na murnar haihuwarsa."

Ministan ya jadada cewa zaman lafiya da tsaro abu biyu ne masu muhimmanci don cigaban tattalin arziki da walwala a Najeriya.

Kirsimeti: Ku yi yi wa kasa addu'a samun zaman lafiya - FG

Ya yi kira ga yan kasar su yi amfani da lokacin bikin su yi wa kasa addu'a don ganin kawo karshen rashin tsaro.

Ya kuma yi kira ga yan Najeriya su bada gudumawa yayin zaben 2023 ta hanyar yin zabe cikin zaman lafiya da kaucewa duk wani abin da zai tada tarzoma.

Aregbesola ya ce gwamnati ta dauki matakan tsare rayuka da dukiyoyin yan kasa kuma tana fatan mutane za su taimakawa jami'an tsaro da bayanai masu amfani.

Kara karanta wannan

Dubbannin Malaman Makaranta a Arewa Sun Yunkuro, Sun Ayyana Wanda Zasu Goyi Baya a 2023

Babban bankin Najeriya ya kara adadin kudin da yan kasa za su iya cirewa duk mako zuwa N500k

A wani rahoto, Bayan korafe-korafe, babban bankin kasa, CBN, ya kara adadin kudin da yan Najeriya za su iya cire wa duk sati zuwa N500,000.000

CBN ya saka dokar kayyade adadin kudin da za a iya cirewa ne duk sati biyo bayan sauyin wasu takardun nairorin kasar a baya-bayan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel