An Tsaida Ranar da Kwankwaso Zai Yi Jawabi a Chatham House, Zai Tallata Manufofinsa

An Tsaida Ranar da Kwankwaso Zai Yi Jawabi a Chatham House, Zai Tallata Manufofinsa

  • Kwanaki kadan bayan Bola Tinubu ya bayyana a dakin taron Chatham House, an gayyaci Rabiu Kwankwaso
  • Sanata Rabiu Kwankwaso mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin inuwar NNPP zai je Birtaniya
  • ‘Dan takaran zai yi jawabi kamar yadda abokan gabarsa a 2023, Atiku Abubakar da Peter Obi za su yi nan gaba

England - Tun da aka kira ‘dan takaran jam’iyyar APC na zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu zuwa Chatham House, aka san za a gayyaci sauran ‘yan takara.

A ranar Alhamis, 22 ga watan Disamba 2022, labari ya zo daga shafin Chatham House Africa a dandalin Twitter cewa za a tattauna da Rabiu Kwankwaso.

Rabiu Kwankwaso wanda ya rike kujerar Sanata tsakanin 2015 da 2019 zai yi bayanin manufofinsa na gyara Najeriya idan ya yi nasarar karbar mulki a 2023.

Kara karanta wannan

‘Yan Kasuwa Na Lissafin Sayen Mai a N148, Tinubu Ya Dage a Cire Tallafin Fetur

Bayanan da Legit.ng Hausa ta samu daga @AfricaProg ya nuna za ayi wannan zama ne a ranar 18 ga watan Junairu 2023, yanzu saura kimanin wata daya.

Za a zauna da 'yan takara

Wannan haduwar da za ayi da tsohon Gwamnan na jihar Kano yana cikin jeringiyar tattaunawar da za ayi da masu neman shugabancin Najeriya a cibiyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron da za ayi nan da kwanaki 26 shi ne zai zama na uku da za a gudanar a cibiyar binciken domin fahimtar yadda zabe mai zuwa zai kasance a kasar.

Kwankwaso
Peter Obi, Kwankwaso da Atiku a 2019 Hoto: www.icriforum.org
Asali: UGC

Masu neman karin bayani a game da yadda tattaunawar za ta kasance, sai su ziyarci shafin cibiyar.

Kwankwaso zai sake barin Najeriya

Ana sa ran ‘dan takaran jam’iyyar adawae ta NNPP zai dauki wasu cikin mukarrabansa zuwa Birtaniya domin amsa goron gayyatar da aka aiko masa.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Shugaban Majalisa da Cin Amanar Tinubu da Yi Wa Atiki aiki a Zaben 2023

Wannan zai zama karo na biyu da Kwankwaso ya kai ziyara zuwa kasar waje a ‘yan makonnin nan. Kwanakin baya shi da mutanensa sun je kasar Amurka.

Chatham House za ta karbi bakuncin APC, PDP, NNPP da LP

Tun a baya an samu labari daga ICRI za a zabi ranaku na musamman da za a warewa manyan ‘yan takaran shugaban kasa a Najeriya domin su tallata kansu.

Baya ga ‘yan takaran=, shi ma shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu zai yi bayanin shirin da suke yi na gudanar da zabe mai nagarta.

Bayan zuwan Bola Tinubu, Darektan sashen harkokin Afrika a Chatham House, Alex Vines ya ce za a saurari Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi.

NNPP ta karbu a Abia

An ji labari Shugaban Kungiyar Abia Christian Community (ACC) ya ce sun yanke shawarar Jam’iyyar NNPP za su zaba a zaben Gwamna da za ayi a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Jita-Jitar Da Ake Yi Cewa Tinubu Zai Musuluntar Najeriya

Apostle Reminder C. Gad wanda shi ne shugaban ACC ya ce za su dage wajen ganin Dr. Ukpai Iro Ukpai ya zama Gwamnan Abia a jam’iyya mai kayan dadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel