Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Jonathan Ya Mika Babbar Lambar Yabo Ga Jigon APC Mai Karfin Fada A Ji
- Goodluck Jonathan, tsohon shugaban Najeriya, ya gabatar da lambar yabo ta Grand Commander of Ebony Hall of Fame (GCEHF) ga tsohon gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti
- Fayemi, yayin wallafa hotunan taron ya ce an karrama shi ne saboda aikin da ya yi na sauya kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, zuwa wata karamar gwamnati na kasa
- Tsohon ciyaman din na NGF ya kuma gode wa gwamna da mutanen Ebonyi saboda karamcin da suka masa
Abakaliki, Ebonyi - Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya gabatar da lambar yabo ta Grand Commander of Ebony Hall of Fame (GCEHF) ga tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi.
Fayemi, wanda jigo ne na jam'iyyar APC ya bayyana labarin a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 23 ga watan Disamba, inda ya wallafa hotunan lokacin da ake bashi kyautan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane lambar yabo Jonathan ya gabatarwa jigon APC, Kayode Fayemi?
Tsohon ciyaman din na kungiyar gwamnonin Najeriya ya ce an bashi lambar yabon ne saboda kokarinsa na sauya kungiyar zuwa wata karamar gwamnati na kasa.
Yayin da ba a iya tantancewa ko ranar Juma'a ne aka bada lambar yabon ba, tsohon ministan ya mika godiyarsa ga gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, bisa karamci da lambar yabon.
Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti wanda sanannen jigon jam'iyyar PDP ne shima ya halarci taron.
Abin da ke faruwa a baya-bayan nan dangane da Fayemi, APC, Goodluck Jonathan, PDP da Ebonyi
An hangi Fayose da Fayemi suna yin musabaha tare da rungumar juna a wurin taron.
Wani sashi na sanarwar ta ce:
"Abin alfahari ne a gari ni in karba lambar yabo ta Granda Commander na Ebony Hall of Fame (GCEHF). Wannan karamawar ta tabbatar da kokarin mu na sauya NGF zuwa wani kungiya da zai zama abin koyi ga kananan gwamnatoci tare da abbataccen sakamako na ci gaba da gudummawar gina kasa."
Ga sakon a kasa:
Asali: Legit.ng