Wata Sabuwar Kungiya Mai Hatsari Ta Ɓullo A Najeriya, Shugaban NSCDC Ya Yi Gargaɗi

Wata Sabuwar Kungiya Mai Hatsari Ta Ɓullo A Najeriya, Shugaban NSCDC Ya Yi Gargaɗi

  • Ahmed Abubakar Audi, kwamanda janar na shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, NSCDC, ya ankarar da yan Najeriya kan bullar wata muguwar kungiya a kasar
  • Audi, yayin jawabinsa wurin taron kwamandojin NSCDC a Abuja ya ce yan kungiyar suna saka kaya irin na jami'an tsaro sannan su rika tada hankalun mutane da kai hare-hare
  • Shugaban na NSCDC ya zubarar da kwamandojinsu su dage wurin tattara bayanan sirri su kuma kare kayayyakin gwamnati da ke yankunansu musamman a halin yanzu da ake fuskantar zabe

FCT, Abuja - Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC), Ahmed Abubakar Audi, ya bayyana cewa akwai wata kungiya mai hatsarin gaske a Najeriya da ke haddasa rikici.

Audi ya bayyana hakan ne yayin bude taron kwamandojin rundunar na shekarar 2022 tare da kwamandojin jihohi a hedkwatar NSCDC a ranar Laraba a Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ayarin Dakarun Yan Sanda Hari a Arewa, An Rasa Rayuka

Shugaban NSCDC
Wata Sabuwar Kungiya Mai Hatsari Ta Bullo A Najeriya, Shugaban NSCDC Ya Yi Gargadi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Audi ya ce an gano kungiyar ne sakamakon bayanan sirri da hukumar ta samu, rahoton Blue Print.

Sabuwar Kungiya Mai Hatsari Ta Bullo, Suna Sanya Kayan Jami'an Tsaro - Audi

Shugaban na NSCDC yayin da ya ke zaburar da kwamandojin hukumar ya ce:

"Akwai wata kungiya mai hatsari a gari. Mambobin na saka tufafi irin na jami'an tsaro kuma sun fara adabar al'umma.
"Don haka dole mu zage damtse mu gane wadannan mutanen."

Ya zaburar da kwamandojin yankuna da jihohi su rika aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar sun kare kayan gwamnati a jihohinsu yayin da ke magana kan hare-haren da ake kaiwa INEC.

Shugaban NSCDC ya bukaci kwamandojin hukumar su kare kayayyakin INEC

Audi ya ce:

"Za mu tuhumi kwamandoji jihohi idan an kai hari a wata cibiyar INEC a jiharsu."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Okupe Yayi Murabus Daga Matsayin DG na Kamfen din Peter Obi

Ya bukaci su mayar da hankali kan tattaro bayanan sirri, yana mai cewa 'kare afkuwar laifi ya fi sauki fiye da magance shi'.

Shugaban na NSCDC ya bukaci kwamandojin yankuna su saka idanu kan tafiyar da jami'ansu, kuma zai rika sauraron bayanai na abin da ke tafiya a karkashin yankinsu duk minti-minti.

Ya bukaci su shirya tarukan kara wa juna ilimi ga jami'ansu don fadakar da su bukatan da ke akwai na biyayya ga dokokin zabe, musamman kamar yadda ya ke a sabuwar dokar zabe.

An yanke wa matashi daurin shekaru 2 a gidan yari saboda lalata allunan tallan kamfen din Atiku

A bangare guda, wata kotu da ke zamanta a Bukuru, jihar Filato ta yanke a wani matashi dan shekara 20, Gabriel Orupou hukuncin daurin shekara biyu a gidan gyaran hali.

Alkalin kotun Hycinth Dolnaan, amma ya bawa Orupou zabin biyan tarar N100,000 bisa laifin da aka same shi da aikatawa na lalata allunan tallar shugabancin kasa na Atiku Abubakar na PDP.

Kara karanta wannan

Zabe ya karaso, Hukumar INEC ta Jero Manyan Abubuwa 2 da take Tsoro a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel