Doyin OKupe Yayi Murabus Daga Darakta Janar na Kamfen din LP

Doyin OKupe Yayi Murabus Daga Darakta Janar na Kamfen din LP

  • Darakta janar na tawagar yakin neman zaben Peter Obi da Dattti Baba-Ahmed, Doyin Okupe, yayi murabus a ranar Talata
  • Ya sanar da hakan ne ta wata wasika da ya aikewa Peter Obi inda yace ya matukar yin kokari wurin kamfen din don haka ba zai so ya rushe ba
  • Ya bukaci a nada sabon darakta janar na tawagar kamfen din wanda zai karba ragamar kuma komai ya tafi lafiya kalau

FCT, Abuja - Doyin Okupe ya yi murabus daga matsayinsa na darakta janar na tawagar kamfen din neman kujerar shugabancin kasa ta Peter Obi da Datti Baba-Ahmed, jaridar TheCable ta rahoto.

Ya sanar da wannan murabus din ne a wasikar da ya aikewa Peter Obi, 'dan takarar kujerar shugabancin kasan Najeriya mai kwanan wata 20 ga Disamban 2022.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Wa Matashi Ɗan Shekara 20 Ɗaurin Gidan Yari A Jihar Arewa Saboda Lalata Allunan Kamfen Ɗin Atiku

Murabus din Okupe yana zuwa ne bayan sa'o'i kadan da kotu ta kama shi da laifin wanke kudin haram tare da aike shi gidan yari.

"Zuwa ga Peter, idan za ka tuna jiya nayi maka bayani kan abinda ya taso nake neman adalci tare da wanke sunanan ta hanyar amfani da tsarin shari'arf Najeriya."

- Wasikar tace.

"Na saka abubuwa da yawa cikin yakin neman zaben ka ta yadda ba zan bar halin da nake ciki ya zamo abun dauke hankali ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A wannan hali, na yanke shawarar janyewa tare da roko a nada sabon darakta janar na kungiyar kamfen din wanda zai iya cigaba da aikin babu dauke hankali."

Murabus din Okupe yana zuwa ne sa'o'i bayan da kotu ta kama shi da laifin wanke kudin sata.

A zaman da babbar kotun tarayyar tayi a ranar Litinin a Abuja, Ijeoma Ojukwu, alkali mai shari'ar ya yankewa Okupe hukuncin shekaru biyu a gidan yari bayan ya kama shi da laifuka 26 daga cikin 59 da ake zarginsa da su daga hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Samu Gagarumar Nasara, Fitaccen Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Amince da Bukatar PDP

Sai dai an bashi zabin biyan N500,000 kan kowanne daga cikin laifukan wanda jimillar kudin ya kama N13 miliyan.

Kotu ta daure Doyin Okupe

A wani labari na daban, wata kotun tarayya dake zama a babban birnin tarayya ta daure Doyin Okupe shekaru biyu a gidan kurkuku.

An kama shi da laifuka 26 wadanda suka hada da wanke kudin haram da satar wasu wadanda suka kai N720 miliyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel