Kotu Ta Yanke Wa Matashi Ɗan Shekara 20 Ɗaurin Gidan Yari A Jihar Arewa Saboda Lalata Allunan Kamfen Ɗin Atiku

Kotu Ta Yanke Wa Matashi Ɗan Shekara 20 Ɗaurin Gidan Yari A Jihar Arewa Saboda Lalata Allunan Kamfen Ɗin Atiku

  • Kotu a yanke wa wani matashi hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari a Plateau kan lalata allon kamfen din Atiku
  • Amma alkalin kotun ya bawa Gabriel Orupou zabin biyan tarar kudi N100,000 a maimakon zuwa gidan gyaran halin
  • Wanda aka samu da laifin ya ce wasu matasa uku ne suka bashi N2,000 suka bukaci ya tafi ya lalata allon kamfen din

Plateau - Wata kotu mai zaman ta a Bukuru karkashin jagorancin Hon Hycinth Dolnaan, a ranar Litinin, ta yanke wa wani dan shekara 20, Gabriel Orupou, daurin shekara 2 a gidan yari tare da zabin biyan takarar N100,000 saboda lalata allon yakin neman zabe na jam'iyyar PDP a Zaramaganda, karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau.

An yanke masa hukuncin ne saboda lalata allon tallar takarar shugabancin kasa na Atiku/Okowa, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Za Mu Fi Maza Tabuka Abin Azo A Gani, In Ji Yan Takarar Gwamna Mata a Najeriya

Hukuncin Kotu
Kotu Ta Ɗaure Ɗan Shekara 20 A Jihar Arewa Saboda Lalata Allunan Kamfen Din Atiku. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda ya ke kunshe cikin rahoton da yan sanda suka gabatar, an gurfanar da Orupou ne kan laifuka masu alaka da hadin baki don aikata laifi wanda suka ci karo da sashi na 59 da 313 na Penal code ta jihar Plateau.

An yi karar Orupou a kotun ne da wasu mutane uku da kawo yanzu ba a kama su ba a cewar rahoton.

Hukuncin kotu

Yayin yanke hukuncin a ranar Litinin bayan samun Orupou da laifi a ranar Juma'a da ta gabata bayan ya amsa laifinsa yayin da dan sanda mai shigar da kara Martina Bitrus ya karanto masa.

Daga bisani, kotun da dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Disamba don yanke hukunci.

Orupou: N2,000 aka biya ni domin in lalata allon kamfen din Atiku

Kara karanta wannan

Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi Zaiyi Zabe A Kurkuki, Sakamakon Umarnin Kotu Na A Tsareshi

Lokacin da aka kira shari'ar, and aka samu da laifin ya nemi afuwa, ya kara da cewa wani Musa, Bash da Danlami suka dauke shi haya suka biya shi naira dubu biyu.

Ana neman mutane ukun a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel