Fitaccen Gwamnan Kudu Ya Saka Wa Filin Wasa Sunan Abacha, Buhari Da Yar Abacha Sun Yi Martani

Fitaccen Gwamnan Kudu Ya Saka Wa Filin Wasa Sunan Abacha, Buhari Da Yar Abacha Sun Yi Martani

  • David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya karrama tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, ta hanyar saka wa filin wasanni sunansa
  • Yar Abacha kuma first lady na jihar Yobe, Gumsu Sani Abacha, ta ce cancanta ne ya saka aka karrama mahaifinta ba neman alfarma suka yi ba
  • Shugaba Muhammadu Buhari ta bakin hadiminsa na bangaren sadarwa na zamani, Bashir Ahmed, ya gode wa jihar bisa wannan karamcin

Abakaliki, Ebonyi - Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya nada wa filin wasa na Ebonyi Olympic Stadium, sunan tsohon shugaban mulkin soja Janar Sani Abacha.

Abacha ne shugaban mulkin soja wanda ya amince da a kirkiri jihar Ebonyi a ranar 1 ga watan Oktoban 1996, The Sun ta rahoto.

Umahi da Abacha
Fitaccen Gwamnan Kudu Ya Saka Wa Filin Wasa Sunan Abacha, Buhari Da Yar Abacha Sun Yi Martani. Hoto: Odogwu
Asali: Twitter

Sanarwar ta ce saka wa filin wasan sunan Abacha wani hanya ne na karrama tsohon shugaban kasar saboda gudunmawar da ya bada don gina jihar.

Kara karanta wannan

"Ban Sani Ba Sai Daga Baya" Gwamnan Arewa Ya Umarci a Hanzarta Sakin Wanda Ya 'Zage' Shi a Soshiyal Midiya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abin da ke faruwa game da Dave Umahi, Sani Abacha, Ebonyi da Muhammadu Buhari a baya-bayan nan

Mataimakin Umahi na musamman kan kafar watsa labarai da tsare-tsare, Chooks Oko, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar bayan taron majalisar zartarwa na jihar.

Yar tsohon shugaban kasar kuma first lady na jihar Yobe, Gumsu Sani Abacha, ta yi martani kan cigaban tana mai cewa iyalan Abacha ba su nemi a musu alfarmar ba.

Ta yi rubutu a shafinta na Twitter tana mai cewa:

"Mun gode wa Allah, babu kamfen babu neman alfarma. Cancanta ne zalla."

Ya ya ke martani kan cigaban, Shugaba Muhammadu Buhari, ta bakin hadiminsa kan sadarwa ta zamani, Bashir Ahmad, ya ya ce, "Mun goda Ebonyi".

Hakazalika, wasu da ke bibiyan shafinta suma sun yi tsokaci ta hanyar taya iyalan murna.

Kara karanta wannan

Allah Yayi wa Alhaji Shehu Malami, Fitaccen 'Dan Kasuwa Kuma Yariman Sokoto, Rasuwa

Martanin yan Najeriya kan saka wa filin wasanni sunan Abacha a Ebonyi

Daya daga cikin masu martanin mai suna @uokacha70, ya ce:

"Ina taya murna ga iyalan wadanda aka karrama.
"Amma a sani babu gini mai wannan sunan a Ebonyi a yanzu. An ware wani fili don gina filin wasannin, don haka hoton da ke jaridar sun newspaper ba a gina shi ba."

Wani mai suna @AEberonwu ya ce:

"Muna taya ki murna. Duk da tsirarun mutanen da ke son bata masa suna, za a rika tunawa da shi saboda ayyukan alheri da ya yi.
"Ebonyi ta fara, saura za su bi sahu. Allah ya jikan Abacha."

Wani dan Najeriya mai suna @ComrSani ya yi tsokaci:

"Wannan kyakyawan misali ne na jarumi da ya rasu tsawon shekaru amma har yanzu ba mu manta da shi ba a zukatan mu."

Adebayo Aroyewun ya bayyana darasi na rayuwa da rahoton yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Saraki @60: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Garzaya Madina Don Godiya Ga Allah

"Haka rayuwa ta ke, ba zai yi wu dukkan mu mu rika barci ta kanmu na kallon gefe guda ba."

Ga rubutun da ta yi a nan:

Fulani da Hausawa Sun Goyi Bayan Takarar Gwamna Ayade

A wani rahoton, al'ummar fulani da hausawa na jihar Ebonyi a karamar hukumar Ogoja sun kai ziyarar goyon baya ga Gwamna Ben Ayade.

Yayin ziyarar, sun fada masa cewa suna goyon bayan takararsa na zama sanata a zaben 2023 kuma za su zabi APC daga sama har kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164