Gwamna Buni Ya Umarci Yan Sanda Su Saki Yaron da Ya Zage Shi a Soshiyal Midiya

Gwamna Buni Ya Umarci Yan Sanda Su Saki Yaron da Ya Zage Shi a Soshiyal Midiya

  • Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya umarci 'yan sanda su gaggauta sakin wanda ake zargi ya zage shi a Soshiyal midiya
  • A kwanakin baya, Mahaifin yaron ɗan kimanin shekara 16 ya yi kira ga hukumomi su taimaka su sako ɗansa
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan abinda ya faru tsakanin wani ɗalibi da Aisha Buhari, uwar gidan shugaban kasa

Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya umarci hukumar 'yan sanda ta gaggauta sakin yaron da ta tsare bisa zargin ya ci mutuncinsa a Soshiyal midiya, kamar yadda Premiumtimes ta rahoto.

Idan baku manta ba mahaifin wanda ake zargi, Mallam Garba Isa, ya shaida wa manema labarai cewa jami'an 'yan sanda sun kama ɗansa ranar 11 ga watan Disamba, 2022.

Gwamna Mala Buni
Gwamna Buni Ya Umarci Yan Sanda Su Saki Yaron da Ya Zage Shi a Soshiyal Midiya Hoto: Mala Buni
Asali: Facebook

Magidancin yace sun cafke yaron ne bisa zargin ya 'zagi' gwamna Buni kuma ya roki mahukunta su yi hakuri su duba yuwuwar sakin ɗansa, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Darusa 10 da Za a Dauka daga Shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara – Kabir Asgar

A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na gwamna Buni, Mamman Muhammed, ya fitar ranar Talata, yace gwamna bai da masaniyar kame da kuma tsare yaron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan ya ce ba dole bane kama duk wanda ya zage shi ko ya ci mutuncinsa ba inda ya ce:

"Wannan abu ne da ya zama ruwan dare a shugabanci kuma mun san haka, saboda haka ba da yawuna ba, ban yarda a tsare kowa ba. Har lokacin da ake bani labari ban san an kama shi an tsare ba."
"A halin yanzu ina mai ba da umarnin a hanzarta sakinsa ya koma gida. Sai dai yana da kyau mu sani, duk da gwamnatin Buni na tafiya a buɗe, gudummuwa da kuma suka abu ne masu ma'ana da ba za'a kauce musu ba."
"Masu amfani da Soshiyal midiya ku sani akwai nauyin da ke kanku, ku girmama kowane mutum, Addini, al'adu, jam'iyyun siyasa musamma a yanzun da muke kakar kamfe."

Kara karanta wannan

“Fatan Zai Saka”: Hamshakin Mai Kudi ya Siya Gwanjon Wando Mai shekaru 165 kan N50m

Yan Sanda Sun Kama Yaro Mai Shekaru 16 kan Zagin Gwamna Buni

A wani labarin kuma Kun ji yadda jami'an yan sanda suka kama ɗan shekara 16 a duniya da zargin ya taba mutuncin gwamnan Yobe

Kwamishinan hukumar 'yan sandan Yobe ya tabbatar da cewa yaron mai suna Umar yana hannunsu a tsare kuma suna shirin gurfanar da shi a Kotu.

Mahaifin yaron ya nemi jami'an yan sanda da mai girma gwamna su yafe wa yaron kana su sake shi ya dawo gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel