Saraki Ya Garzaya Kasa Mai Tsarki Don Nuna Godiya Ga Allah Yayin da Zai Cika Shekaru 60 a Duniya
- Abubakar Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, zai cika shekaru 60 a gobe Litinin
- Saraki ya tafi kasar Saudiyya domin yin Umara tare da godiya da wannan ni'ima da Allah ya yi masa
- Masoya sun taya dan siyasar murna da fatan alkhairi, inda wasu da dama suka ce suna kewarsa a majalisa
Saudiyya - A ranar Litinin, 19 ga watan Disamba ne tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki zai cika shekaru 60 a duniya.
Domin raya wannan rana, Saraki ya garzaya kasa mai tsarki don nuna godiya ga Allah madaukakin sarki.
Saraki ya rubuta a shafinsa na Facebook:
"Nan da 'yan awanni zan cika shekara 60 a duniya, bisa haka ne na zo birnin Madinah domin yin godiya ga Allah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ko ba komi, yayin da Allah ya tambaye mu a littafinsa mai tsarki, cikin Surah Ar-Rahman da cewa; "Wanne daga ni'imomin Mahaliccinku ku ke ƙaryatawa? Amsarmu ita ce, BABU!"
Jama'a sun yi martani
Yusuf Bayero ya yi martani:
"Allah ya karba shugaban majalisar dattawa da ya fi kowanne a tarihi Najeriya ina yi maka fatan samun tsawon rayuwa, wadata da kariyar Ubangiji."
Nazir Kabir Hali ya ce:
"Allahu Akba Lallai Sir Kayi Tunani KumaAllah Ysm Sauran Rayuwarka Albarka Ys Ka Cira Duniya Da Lahira Don Annabi Da Al-Qur'ani."
Abdurrahman Mukhtar Tody ya ce:
Masha Allah. Allah qaro masu Albarka, Gaskiya muma Allah ubangiji ya Mana Arziqi."
Suleman Umar Hussain ya ce:
"Allah ya kara shekaru masu albarka, mun yi kewar shugabancinka a majalisar dattawa, yanzu muka san muhimmancin rashinka, Allah ya karo albarka yallabai."
Garba Mustapha ya ce:
"Masha ALLAH Najeriya na kewarka a matsayin shugaban majalisar dattawa saraki."
Muntari Rabi'u Bichi ya yi martani:
"Masha Allah. Alhamdulillah. Allah ya Karo Ma Su Albarka."
Buhari @80: Hadimin Tinubu ya taya shugaban Najeriya murnar zagayowar haihuwarsa
A wani labarin, a ranar Asabar, 17 ga watan Disamba ne shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya cika shekaru 80 a duniya.
Domin raya wannan rana, hadimin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na aPC, Joe Ibokwe ya yi shagube ga abokan adawar Buhari.
Ya ce duk da rade-radin ake ta yi cewa ya mutu, yau ga shi Allah ya raya shi har ya kai shekaru 80 a duniya.
Asali: Legit.ng