Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram Da Dama a Jihar Borno

Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram Da Dama a Jihar Borno

  • Sojojin Najeriya sun samu gagarumin nasara a kan mayakan Boko Haram yayin wani arangama da suka yi a yankin Mafa da ke jihar Borno
  • A yayin fafatawa tsakanin sojoji da Boko Haram, dakarun Operation Hadin Kai sun halaka mayakan kungiyar ta'addancin masu yawan gaske
  • Sojoji sun yi nasarar kama wani dan ta da kayar baya daya yayin da wasu suka tsere da raunin harbi

Borno - Dakarun Operation Hadin Kai da ke yaki da ta'addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun kashe mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram da dama a yayin wani arangama da suka yi a Ngowom da ke karamar hukumar Mafa ta jihar Borno.

An kashe yan ta'addan ne yayin da suke jerin gwano a kan wasu babura 20 daga yankin arewacin jihar zuwa yankin Mafa, a hanyarsu ta zuwa dajin Sambisa.

Kara karanta wannan

Kaduna: ‘Yan Chana da Suka yi Wata 6 Hannun Masu Garkuwa da Mutane Sun Shaki Iskar ‘Yanci

Jihar Borno
Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram Da Dama a Jihar Borno Hoto: The Cable
Asali: UGC

Sojoji sun shiga aiki bayan samun bayanan sirri

Wasu majiyoyi na sirri sun sanar da Zagazola Makama, kwararre a kan tsaro a tafkin Chadi cewa sojojin sun samu nasarar ne yayin da suke aiki kan wani bayanan sirri da suka samu cewa yan ta'addan na hanyar zuwa yankin Mafa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dakarun da hadin gwiwar yan sa-kai na CJTF sun kai ma yan ta'addan kautan bauna kuma nan take suka kashe da yawansu.

An kama dan ta'adda daya da ransa

Zagazola Makama ya kuma rahoto cewa dakarun sojin sun kama wani dan ta'adda da ransa yayin da sauran suka tsere da raunukan bindiga.

Majiyar ta ce:

"Kautan baunan ya yi sanadiyar yin musayar wuta tsakanin mu. Daga bisani sun janye sannan suka yi kokarin guduwa amma muka fatattake su kuma sakamakon haka, mun kashe da yawansu. Wasu da dama sun tsere da raunin harbi."

Kara karanta wannan

Zakakuran Soji sun Kai Farmakin Kwantan Bauna, Sun Sheke ‘Yan Ta’adda 4 a Borno

Ya yi bayanin cewa mambobin CJTF biyu sun jikkata a yayin zazzafan musayar wutan yayin da aka kwato makamai da babura daga wajen yan ta'addan.

Ya kuma ce:

"Dakarunmu na Ngowom karkashin Mafa sun karbo babura biyu da bindigar toka daya."

Yan sanda sun gano masana'antar kera bama-bamai a Najeriya

A wani labari na daban, rundunar yan sanda a jihar Ebonyi ta ce jami'anta sun yi nasarar kai samame wani wurin kera bama-bamai a jihar ta kudu maso gabas.

An zargi kungiyar yan awaren IPOB da gudanar da haramtaciyyar masana'antar a boye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel