Matar Aure Ta Fito Fili Ta Roki Budurwar Mijinta Ta Dawo Cikin Rayuwarsu, Ta Ce Ta Rasa Nutsuwa a Gidanta

Matar Aure Ta Fito Fili Ta Roki Budurwar Mijinta Ta Dawo Cikin Rayuwarsu, Ta Ce Ta Rasa Nutsuwa a Gidanta

  • Wata kyakkyawa matar aure ta fito fili ta nemi abokiyar alfashan mijinta ta dawo gareshi saboda wasu matsalolin cikin gida
  • Matar cikin barkwanci ta yada yadda mijinta ya shiga wani hali tun bayan da budurwar ta daina turo masa sakon tes
  • Yayin yada bidiyon, ta ce a yanzu dai bata cikin kwanciyar hankali tun bayan da budurwar ta daina mu’amala da mijinta

Matar aure, Busisiwe Isaacs ta ba da mamaki yayin da ta yada wani bidiyon neman budurwar mijinta ta dawo gareshi saboda halin da mijin ke ciki a yanzu.

Matar ta bayyana cewa, mijinta ya sauya matuka ainun tun bayan da budurwar ta fita daga rayuwarsa, ta daina turo masa sakwanni.

A cikin bidiyon, an ga lokacin da matar ke rokon budurwar da ta ci gaba da turo ma mijinta sakon tes ko za ta samu sukuni a cikin gidan aurenta.

Kara karanta wannan

"Ku Wuce Ɗaki": Wani Mutumi Ya Sunkuci Matarsa Yayin da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Bidiyon Ya Ja Hankali

Matar aure ta roki budurwar mijinta ta dawo gasreshi
Matar Aure Ta Fito Fili Ta Roki Budurwar Mijinta Ta Dawo Cikin Rayuwarsu, Ta Ce Ta Rasa Nutsuwa a Gidanta | Hoto: @busisiweisaacs/TikTok, Jonathan Knowles/Getty images
Asali: UGC

A kalamanta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Zuwa ga budurwar da ta daina turo sakon tes ga miji na, na gaza gane kansa tun da kika tafi. Ban san zaman lafiya tun da kika tafi.”

Kalli bidiyon:

Martanin jama’ar TikTok

Jama'ar TikTok sun yi martani mai ban mamaki tun bayan ganin wannan bidiyo mai ban dariya.

@kedidinne:

“Har zuciyarsa yana son fada miki amma nauyi yake ji.”

@sibongilemokoena12:

“Kada ki taba raina tasirin ‘yan matan waje.”

@nomso80:

“Matukar hakan abin dariya ne, gida yakan zamakamar makabarta idan miji yana irin haka, ina magana ne daga bin da ya faru dani.”

@jovonnearizonafiredavis:

“Na ga abokin aiki na magidanci na tsawon shekaru 25 da ya shiga damuwa saboda budurwarsa ta shekaru 9.”

@conny_147:

“Mahaifiyata tace lokacin da mahaifina ya rabu da budurwarsa dawowa gida ya yi yana kuka kamar karamin yaro ya ma gaza fita daga motarsa.”

Kara karanta wannan

Yadda Yan Najeriya Suka Share Hawayen Wata Dattijuwa Da Ke Kwana a Titi, An Sama Mata Muhalli

@mariekiplimo1:

“Ka’ida daya ce a cikin gida na, idan rikici da budurwarsa to ba ya dawowa gida har sai ya daidaita komai.”

Daga dauko karuwa, ta jefa shi a matsala

Magidanci ya shiga tashin hankali bayan da ya dauko karuwa ya kawo gidan abokinsa, ta sace wata sarka mai darajar akalla Naira miliyan 6.

Abokin dai ya fusata ta kama motar wannan magidanci, yace ko dai ya biya shi ko kuma ya ci gaba da rike mota.

Mutane da dama sun bayyana martaninsu kan wannan lamari, sun ce ya yi ganganci, hakan ya kamata ya faru dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel