Yan Najeriya Sun Yiwa Wata Tsohuwa Mara Galihu Sha-tara Ta Arziki, Bidiyon Ya Yadu

Yan Najeriya Sun Yiwa Wata Tsohuwa Mara Galihu Sha-tara Ta Arziki, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata dattijuwar mata mara galihu ta samu kyautar kudi naira miliyan biyu daga wasu yan Najeriya
  • Da farko an gano matar a wani bidiyo da ya yadu a yakune kamar mai yunwa sannan tana kwana ne a kan titi
  • Wani shahararren matashi a Instagram, Tunde Ednut ya wallafa bidiyonta inda ta ja hankalin yan Najeriya da suka cika da tausayinta

Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuno lokacin da wata dattijuwar mata yar Najeriya ta samu taimako daga wajen yan Najeriya.

Shafin @ositapopcorn ne ya wallafa bidiyon a Instagram, inda ya rahoto cewa matar ta samu kyautar gida da zunzurutun kudi fiye da naira miliyan biyu.

Dattijuwa
Yan Najeriya Sun Yiwa Wata Tsohuwa Mara Galihu Sha-tara Ta Arziki, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @ositapopcorn
Asali: Instagram

Bata da muhalli

Da farko an gano matar a wani tsohon bidiyo da shahararren matashi a Instagram, Tunde Ednut ya wallafa a shafinsa.

Kara karanta wannan

Hazikar ‘Yar Najeriya ta Hada Bulawus Tsuleliya da Ledojin Fiyo Wota, Hotunan Sun Birge

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya sake wallafa bidiyon, sai ya ja hankalin yan Najeriya da dama wadanda suka yi martani ta hanyar yi mata karo-karon kudi fiye da naira miliyan biyu da kuma gida.

A lokacin da @osutapopcorn ya gabatarwa da dattijuwar da kyaututtukan, ta cika da farin ciki sannan ta shiga mamakin ita ce Allah ya kawowa mafita haka.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Odunayo_tayo ta ce:

"Kawai ka saurari turanci mai kyau da take zubawa."

F.lurin ta ce:

"Ohh Allah na, zan so na zama alkhairi ga wannan mata, dan Allah ku tura mun lambar asusun bankinta."

Omalians_crib ta ce:

"Zan so taimakawa wannan matar."

@afoodiesdiaryng ta ce:

"Mama na da karfin imani, komai zai wuce mama."

@abilajih ta ce:

"Tana magana da turanci mai kyau kamar baturiya. Allah ya albarkaci zuciyarki."

@rachiebeautyartistry ta ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon Cikin Dankareren Gidan Da Wani Matashi Ya Kerawa Kansa, Ya Ji Kayan Alatu Kamar Fadar Sarki

"Allah ya shige mata gaba a lamuranta."

@unedited 01 ya yi martani:

"Kasar nan ya kai kowa kasa. Ina rokon Allah yasa kowa ya tsallake shi."

Cikin budurwa ya 'duri ruwa bayan mahaifiyarta ta karbi wayarta tare da duba hirarta

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta yi zuru-zuru a zaune cikin tashin hankali bayan mahaifiyarta ta karba wayarta tare da duba hirarta da saurayinta.

An gano matashiyar ta yi tagumi yayin da uwar tata ta dunga shiga lungu da sako na wayarta kamar wata yar doka da ke binciken mai laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel