Ku Yi Koyi Da Buhari, Gambari Ya Fada Wa Ma'aikatan Gwamnati

Ku Yi Koyi Da Buhari, Gambari Ya Fada Wa Ma'aikatan Gwamnati

  • Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya yi kira ga ma'aikatan gwamnati su yi koyi da Shugaba Buhari
  • Gambari ya yi wannan kiran ne yayin jawabin da ya yi wurin kaddamar da dakin taro da gyaran asibiti da Buhari ya yi a fadar gwamnati
  • Farfesa Gambari ya yaba da salon shugabancin Buhari wanda ya ce ya kuduri aniyar barin Najeriya fiye da yadda ya tarar da ita

Abuja - Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya bukaci ma'aikatan gwamnati su yi koyi da Shugaba Muhammadu Buhari wurin samar da ababen more rayuwa da karfafawa ma'aikata gwiwa don yin ayyukansu, rahoton Daily Trust.

Gambari ya bayyana hakan ne lokacin da ya kaddamar da cibiyar bada horaswa mai wurin zaman mutum 54 wacce aka kawata da na'urorin sadarwa na zamani da sabbin motoccin asibiti uku da gyara da aka yi a asibitin fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, a Abuja.

Ibrahim Gambari
Ku Yi Koyi Da Buhari, Gambari Ya Fada Wa Ma'aikatan Gwamnati. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yaba da salon shugabancin shugaban kasar, yana mai cewa za a rika tunawa da shugaban kasar saboda ya bar tarihi na jogaranci a aikace da nagarta, rahoton New Telegraph.

Buhari ya kudiri niyyar barin Najeriya fiye da yadda ya same ta - Gambari

A cewar shugaban fadar ma'aikatan, Shugaba Buhari ya kuduri aniyar barin Najeriya fiye da yadda ya tarar da ita.

Ya ce:

"Idan kowa ya yi iya kokarinsa don inganta abin da ya tarar, a lokacin da shugaban kasa zai bar ofis a karshen wa'adinsa, zai bar abubuwa fiye da yadda ya tarar da su."

Yayin da ya ke yaba cigaba da aka samu a asibitin, Gambari ya ce gyara sashin asibitin da aka yi zai inganta ayyukan ma'aikata da sauran masu ziyartar asibitin.

Ya kuma jinjinawa Shugaba Buhari saboda ya karfafawa ma'aikatan fadar gwamnati da dukkan ma'aikatun gwamnati gwiwa su gudanar da aiki gwargwadon iyawarsu.

Gambari ya bayyana wata halayyar Shugaba Buhari da ba kowa ya sani ba

A wani rahoton, Ibrahim Gambari ya ce shugaba Muhammadu Buhari mutum ne da ke sakawa biyayya.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a wurin wani taro da aka yi na zagayowar ranar haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel