Gambari ya Bayyana Wata Halayyar Buhari Mai Bada Mamaki

Gambari ya Bayyana Wata Halayyar Buhari Mai Bada Mamaki

  • Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Ibrahim Gambari, ya bayyana cewa Buhari yana sakawa duk wanda yayi masa biyayya
  • Ya sanar da cewa, koda yake shugaban ma’aikata, aiki da biyayya tare da goyon baya yafi amfani, shugaba 1 ne wato shugaban kasa
  • Gambari yace Buhari ya san kimar duk wanda yayi masa abinda ya dace, shiyasa ya sake zakulo shi bayan ministansa da yayi a 1985

FCT, Abuja - Ibrahim Gambari yace shugaban Kasa Muhammadu Buhari Shugaba dake sakawa biyayya, jaridar TheCable ta rahoto.

Ibrahim Gambari
Gambari ya Bayyana Wata Halayyar Buhari Mai Bada Mamaki. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

TheCable ta rahoto cewa, Gambari wanda shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a wani taro da aka yi na cikarsa shekaru 78 a duniya a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Labarin Shiga Shi’a: Jarumin Barkwanci Ali Artwork Yayi Bayani Dalla-dalla

Halascin da Buhari yayi min, Gambari

“A lokacin da na fara aikin, nace aikina mai sauki ne - in yi biyayya, in iya aikina kuma in goyi baya, wannan shiyasa ko shugaban kasa ya ganni ya kira ni da shugaban ma’aikata, ina amsawa da na’am Yallabai.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Yace.

“Amma ana jaddada wajen ma’aikatan ba wai shugaban ba, saboda shugaba daya ne kuma shine shugaban kasa, kuma aikinmu ne mu goyi bayansa cike da biyayya da iya aiki.
“A lokacin da shugaban kasa ya bani aikin nan, ya fito da wani hoto da ka dauka a watan Yunin 1985; a taron OAU ne. Shugaban kasan lokacin yana zaune a tsakiya sai babban sakataren yada labaransa, Wada Mada yana zaune a dama.
“Sai yace: ‘ka tuna wannan hoton? Nace ‘a’a Yallabai, amma na tuna taron’. Yace: “Kai ne Ministan harkokin waje na. An kore mu daga gwamnati a 1985; Bayan shekaru 35 na samu damar dawo da kai.’

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Baiwa Ta Hannun Damansa Wani Babban Muƙami a Gwamnatinsa

“Yace ‘a lokacin an katse mu kuma yanzu na dawo da kai ne domin mu cigaba daga inda muka tsaya. Sai na yi masa godiya kuma sai nace zan iya samun hoton nan ko wankewa in yi? Sai yace a’a, ajiye nawa nayi, kaima je ka nemo naka.
“Dalilai uku suka sa na manna hoton a gaban ofishina. Na farko in tuna muhimmin lokacin rabuwa, in nuna irin halaccin shugaban kasa. Baya manta wadanda suka yi aiki da shi, suka bauta masa da biyayya kuma yake da kwarin guiwa a kansu. Wasu na mora amma su watsar, ban da shi.”

Buhari ya Nada Gambari Matsayin shugaban ma’aikatan Fadarsa

Bayan rasuwar Malam Abba Kyari, shugaban kasa ya nada Ibrahim Sulu Gambari matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadarsa.

Malam Abba Kyari ya rasu ne sakamakon cutar koroba da ta kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel