Matar Aure ta Bayyana Bidiyon Yadda Ta Sukurkuce Bayan Aurent, a baya ‘Yar Kwalisa ce

Matar Aure ta Bayyana Bidiyon Yadda Ta Sukurkuce Bayan Aurent, a baya ‘Yar Kwalisa ce

  • Wata matar aure ta wallafa bidiyo mai taba zuciya domin nuna yadda ta koma bayan wahalar aure da ta sha ta koshi
  • A wani bidiyo da ta Ify Goddy Godwin ta wallafa a TikTok, ta bayyana kyan ta a baya da irin dirarriyar surarta kafin tayi aure
  • Bayan an wallafa gajeren bidiyon a ranar 22 ga watan Nuwamba, tuni ya karade soshiyal midiya inda ake ta tsokaci kan canjinta

Wata mata da take kokarin tsinke igiyar aurenta ta wallafa bidiyo a TikTok domin nuna yadda ta sukurkuce tare da susucewa sakamakon ukubar da ta sha a wurin mijinta.

Daga yar gayu zuwa gaja
Matar Aure ta Bayyana Bidiyon Yadda Ta Sukurkuce Bayan Aurent, a baya ‘Yar Kwalisa ce. Hoto daga TikTok/@ifygoddygodwin
Asali: UGC

Ify Goddy Godwin ta wallafa bidiyon a ranar 22 ga watan Nuwamba inda take nuna irin dirarriyar surarta kafin ta auri mijinta.

A bidiyo mai dauke da hoto daya kacal, Ify ta bayyana a ciccike kuma cikin shiga mai kyau sannan farin ciki bayyane a tare da ita.

Sai dai a wani hoton, surar Ify ta sukurkuce tare da susucewa kuma an gan ta tana razgar kuka a daya daga cikin bidiyoyin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ify tace ta hakura da auren inda ta zargi mijinta da kasancewa mugu wanda bai sauke nauyinsa ba wanda hakan ne yasa ta sukurkuce.

A kalamanta:

“Ina da shi. Ban bata lokaci ba, amma kafin nan na haifa angel. A halin yanzu ita ce kwarin guiwa ta”

Auren ya samar da diya daya wacce ta kira da angel. Gajeren bidiyon mai dauke da sakonni ya janyo maganganu kala-kala a sashen tsokaci.

Kalla bidiyon a kasa:

Martani daga ma’abota amfani da TikTok

Ma’abota amfani da TikTok tuni suka garzaya sashen tsokaci inda suke ta karawa matashiyar kwarin guiwa kan ta daure saboda diyar da ta haifa. Ga wasu daga cikin tsokacin:

@kofoworola234 ya ce:

“Kai maza! Kada ki damu, ki kasance mai kwarin guiwa saboda diyar ki.”

@olaolu Joshua yace:

“Wayyo Allah. Tsorona shi ne kada in saka mace nadamar zama da ni. Ba zan dora laifin a kan namijin ba a yanzu. Ta yuwu rayuwa ce ta juya mishi amma kuma macen bata cancanci wulakanci ba.”

@gracy tayi martani:

“A saboda haka ne nake tsoron aure.”

Matar Aure ta halaka sirikarta don ceto aurenta

A wani labari na daban, matar aure mai zama a jihar Nasarawa mai suna Rosemary Osegba Clem, ta ce bata dana sanin halaka sirikarta mai suna Ashi Clem a yankin Abena da ke karamar hukumar Doma ta jihar.

Abun ya faru ne a ranar 18 ga watan Maris bayan matar auren ta zargi sirikarta da shiga lamurran aurenta.

A wata tattaunawa da Rosemary tayi da jaridar The Nation, ta ce ita da Abaagu Clem sun yi aure ne tun a watan Fabrairun 2016 amma har yanzu babu haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel