Na kashe ta ne don ceto aurena - Cewar matar da ta kashe surikarta

Na kashe ta ne don ceto aurena - Cewar matar da ta kashe surikarta

- Wata matar aure mai zama a jihar Nasarawa mai suna Rosemary ta ce bata nadamar halaka sirikarta

- Kamar yadda ta ce, tun kafin ta auri mijinta, akwai kiyayya mai karfi tsakaninta da mahaifiyarshi wacce hakan yasa ta kasheta don kada ta kashe mata aurenta

- Clem mai shekaru 43 ya bayyana cewa mahaifinshi ya mutu tun yana 18 don haka ba zai dauka lamarin da sauki ba

Wata matar aure mai zama a jihar Nasarawa mai suna Rosemary Osegba Clem, ta ce bata nadamar kashe sirikarta mai suna Ashi Clem a yankin Abena da ke karamar hukumar Doma ta jihar. Lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Maris bayan matar auren ta zargi sirikarta da shiga lamurran aurenta.

A wata tattaunawa da Rosemary tayi da jaridar The Nation, ta ce ita da Abaagu Clem sun yi aure ne tun a watan Fabrairun 2016 amma har yanzu babu haihuwa.

Kamar yadda Rosemary ta ce, ita da sirikarta sun kasance makiyan juna tun ranar da Clem ya nuna ta a matsayin wacce yake so ya aura.

Rosemary ta ce sirikarta tayi iyakar kokarinta wajen tabbatar da cewa Clem bai aureta ba amma sai da aka yi auren.

Ta zargi cewa aurenta da Clem yayi ya hana mahaifiyar shi sakat kuma ta sha alwashin tarwatsa auren.

Rosemary ta ce sirikarta ba ta boye kiyayyarta saboda abu kadan ke saka su fada har da dambe.

Kamar yadda ta kara da cewa, rashin haihuwarta kuwa ya kara kawo matsala daga sirikarta don ta fara maganar cewa dan ta zai karo aure. Mijinta kuwa ya fara biyayya ga shawarar mahaifiyar shi don an hada shi da wata yarinya. Wannan kalubalen ne yasa ta halaka sirikar don ba za ta iya jure ganin wata mace tare da mijinta ba.

KU KARANTA: Hanyoyin da Najeriya ke bi wajen hana yaduwar Coronavirus abin burgewa ne - Majalisar Dinkin Duniya

A ranar Asabar, 18 ga watan Maris ne Rosemary ta samu gatari wanda tayi amfani da shi wajen kashe tsohuwar.

A tattaunawar da aka yi da wacce ake zargin, ta bayyana cewa a shirye take don fuskantar komai kuwa.

"Sirikata ta tsawwala min saboda bana haihuwa. Tun da nayi aure hankalina bai kwanta ba. Duk abinda zai sa in bar gidan tana yi amma na ki tafiya.

"Ta jaddada cewa sai na bar gidan don danta ya karo wata. Ta samo mishi wata yarinya. Duk da akwai laifin mijina da yake sanar mata duk abinda ya faru tsakaninmu, amma ta tsaneni. Yana fada mata cewa bana bashi hadin kai duk da ya san ni ba irin matan da ke son jima'i bace koda yaushe.

"Iyayena duk sun mutu. Idan ya koreni ina zan nufa? Bani da matsala da shi, mahaifiyar shi ce ta saka ni gaba."

A bangaren mijin mai shekaru 43 wanda shi kadai iyayen suka haifa, ya ce maraya ne shi tun yana da shekaru 18. Ya matukar razana da dimauta a kan lamarin saboda kaunar mahaifiyar shi da yake yi.

"Mahaifiyata ba muguwa bace kamar yadda take fada. Ina yawan cewa ta kwantar da hankalinta. So take in yi fada da mahaifiyata saboda ita? Yanzu da ta kashe mahaifiyata, ba zan kyaleta ba." Ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel