Matashiya Yar Najeriya Ta Jinjinawa Surukarta Mai Tsananin Kaunarta A Wani Bidiyo Da Ya Yadu

Matashiya Yar Najeriya Ta Jinjinawa Surukarta Mai Tsananin Kaunarta A Wani Bidiyo Da Ya Yadu

  • Wata matashiya yar Najeriya ta yi jinjina ga uwar mijinta wacce ke nuna mata so da kauna tun bayan da ta auri danta
  • A wani bidiyo mai tsuma zuciya, matar wacce ke cike da farin ciki ta tarbi surukar tata wacce ta kawo mata kayan amfani tuli guda
  • Yayin da take wallafa bidiyon a TikTok, matashiyar ta bayyana cewa matar na kula da ita tamkar yadda take kula da danta

Wata matashiya yar Najeriya mai suna Prettysylver1 a TikTok ta wallafa wani bidiyo mai tsuma zuciya na kyakkyawar uwar mijinta.

Yayin da take wallafa bidiyon, matashiyar ta nuna tsantsar kauna ga dattijuwar matar sannan ta bayyana yadda take bata kulawa.

uwar miji, suruka da danta
Matashiya Yar Najeriya Ta Jinjinawa Surukarta Mai Tsananin Kaunarta A Wani Bidiyo Da Ya Yadu Hoto: @prettysylver1/TikTok
Asali: UGC

A cikin daddadan bidiyon,, an gano lokacin da surukar ta iso gidanta sannan suka rungume junansu cikin tsantsar kauna.

Kara karanta wannan

Har Ta Gaji? Jinjira Yar Kwana Daya Ta Yi Murtuk Da Fuska, Yanayinta Ya Ba Da Mamaki

Matashiyar ta bayyana cewa matar na bata kulawa sosai kamar yadda take kula da danta tun bayan da suka yi aure.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Baku fada mun cewa iyayen miji na da dadi haka ba. Ina son yadda take kaunata. Ta yaya mutum zai zama mai dadin sha'ani haka? Kamar danta," cewarta.

Jama'a sun yi martani

@queenzlyn ta ce:

"Lallai Allah ya yi maki gamon katar a rayuwar nan, yar'uwa ki ci gaba da godema Allah."

@oliviadaniels119 ta rubuta:

"Suna da shi faaa saboda ta amshe ki ne faaa kuma kema kina sonta."

@ayesanty21 ta yi martani:

"Sak surukata faa, tana sona da kula dani kamar danta."

@wealthy_pretty ta yi martani:

"Kin yi dacen samun suruka tagari."

@joeramsey08 ya rubuta:

"Tana kaunar matar ne shi yasa take samun irin wannan kulawar. Wasu matan suna fara kin uwar mijinsu tun kafin su auri danta."

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Yi Bidiyon Wani Gida Mai Daki 1 Da Za a Bayar Haya Kan N1m A Abuja, Jama'a Sun Yi Martani

Kalli bidiyon a kasa:

Surukar ta yiwa matar danta sha-tara ta arziki

A wani lamari makamancin wannan, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wata mai suna @oliviawhitehairs ta garzaya soshiyal midiya don bayyana cewa ta samu mutuniyar kirki a matsayin suruka yayin da ta wallafa bidiyon tarin alkhairin da ta yi mata.

A bidiyon da ta wallafa a TikTok, matar ta yi murna cewa uwar mijinta ta zo daga kauye sannan ta kawo mata kayan abinci dangin su kifi, shinkafa, ayaba da dai sauran kayan amfanin gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel