EFCC Ta Kama Matashi Dan Shekara 19 da Laifin Damfarar ’Yar Kasar Burtaniya £450,000

EFCC Ta Kama Matashi Dan Shekara 19 da Laifin Damfarar ’Yar Kasar Burtaniya £450,000

  • Wani matashi dan Najeriya ya yi amfani da dabara wajen raba wata mata 'yar kasar Burtaniya mai suna Christine Brown
  • Matashin ya amsa laifinsa, ya kuma bayyana abin da ya siya da kudaden da ya karba daga hannun wannan mata
  • Tuni EFCC tace tana ci gaba da bincike, kuma za ta gurfanar da matashin mai suna Endurance idan an kallama binciken

Benin - Hukumar yaki da cin hanci da ta EFCC ta bayyana kame wani matashi mai shekaru 19, Iredia Endurance bisa zargin aikata damfara.

A cewar hukumar, ana zargin Endurance ne da damfarar wata mata mai suna Christine Brown ‘yar kasar Burtaniya kimanin kuadade £450,000.

EFCC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda tace ofishinta na garin Benin ya gurfanar da matashin a madadin Christine.

Kara karanta wannan

Cristiano Ronaldo Ya Samu Sabon Kulob, Inda Zai Rika Samun N90bn a Duk Shekara

An kama matashi bisa laifin sata a kasar waje
EFCC Ta Kama Matashi Dan Shekara 19 da Laifin Damfarar ’Yar Kasar Burtaniya £450,000 | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ta yaya matashin ya samu damar karbar kudade masu yawa haka?

Hukumar a shafinta na Twitter ta ce, matashin ya amsa karbar kudaden ta Bitcoin da kuma takardun kyauta na ‘gift card’, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar hukumar:

“Ofishin shiyya na hukumar EFCC ya kame wani matashi Iredia Endurance bisa zargin aikata damfara.
“Endurance, wanda ya yi ikrarin shi dan shekara 19 ne ya shiga hannun hukumar ne bayan da wata Christine Brown ‘yar kasar Burtaniya ta shigar da karar ya damfare ta 450,000.00.
“Bayan kama shi, matashin ya amsa karbar £250,000.00 daga matar a Bitcoin, FedEx da takardun kyauta. Game da me ya yi da kudin, matashin ya ce ya karkasa kudaden ne a sayen motoci, sarkan zinare, filaye da dai sauransu.
“Kadan daga abubuwan da aka kwato daga hannun matashin sun hada da wayoyin hannu, na’urar tafi da gidanka, layukan waya da fili. Wanda ake zaefin zai gurfana a gaban kotu da zarar an kammala bincike."

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Cukuikuyi Matashin Yana Tuka Ferrari ta Bogi, Zasu Gurfanar Dashi

A watan Oktoba, hukumar 'yan sandan kasa da kasa ta ce, damfara ta yanar gizo na daya da cikin manyan kalubale da hukumomin tsaro ke fuskanta a Afrika, rahoton TheCable.

Hakazalika, hukumar ta ce, karuwar kamfanonin kudi a nahiyar na kara yawaitar laifukan da suka shafi rashawa da damfara.

Dan takarar sanata AA Zaura ma na fuskantar zargi kan damfara, a halin yanzu ana ci gaba da dambarwa kan zargin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel