‘Yan Sanda Sun Cafke Matashi Bayan an Kama Shi Yana Tuka Ferrari ta Bogi

‘Yan Sanda Sun Cafke Matashi Bayan an Kama Shi Yana Tuka Ferrari ta Bogi

  • Rundunar ‘yan sandan kasar Italiya sun cafke wani matashi mai shekaru 26 saboda yana tuka mota kirar Ferrari F340 ta bogi
  • Matashin mai hazaka ya sauya kirar motar Toyota MR2 Coupe zuwa Ferrari din wacce zata kai tsadar £180,000
  • ‘Yan sandan sun ce ya zama dole ne a kare tambarin kamfanin tare da gujewa yin ta bogin bayan sun yi suna a duniya

Italiya - ‘Yan sandan kasar Italiya sun kama wani matashi mai shekaru 26 kan tuka mota kirar Ferrari F430 amma ta bogi.

Fake Ferrari
‘Yan Sanda Sun Cafke Matashi Bayan an Kama ashe Yana Tuka Ferrari ta Bogi. Hoto da punchng.com
Asali: UGC

Kamar yadda The Sun UK suka rahoto, mutumin da ba a bayyana sunansa ba, ya mayar da motarsa kirar Toyota MR2 Coupe zuwa wata mota da tayi kama da Ferrari F430.

A wani bidiyon da yayi yawo a dandalin sada zumunta a ranar Litinin, an ga ‘yan sanda sun tasa keyar mutumin dake cikin motar.

Kara karanta wannan

Qatar ta fi Ingila dadi: Matan turawa sun ce hana shan barasa a 'World Cup' ya sa ba a hantararsu

Motar bogin ta mallaki wasu sassan asalin kirar Ferrari din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zarginsa ne da yin amfani da tambarin su ba tare da izini ba bayan mai magana da yawun ofishin gurfanarwa na Asti ya kai rahoto, jaridar Vanguard ta rahoto.

An fara kera Ferrari F340 tsakanin shekarar 2004 zuwa 2009 kuma kudinta zai kai £180,000.

Mai magana da yawun Guardia di Fianza na kasar Italiya a wata takarda yace:

“‘Yan sandan sun aiwatar da aikin ne karkashin jagorancin masu gurfanarwa na Asti.
“Amfanin hakan shi ne bai wa kamfanin kariya ballantana a wannan lamarin da suka jajirce wurin kawo kaya masu inganci kuma an sansu tare da yabawa duk wani tambarinsu a duniya.”

An kama sojan gona a Legas, Yana satar kayan jama’a

A wani labari na daban, ‘yan sanda a jihar Legas sun yi ram da wani matashi dake ikirarin yana aiki da rundunar sojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 15, Sun Kama ‘Yan Bindiga 7

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya sanar da kamen Andy Edward mai shekaru 39 dauke da kayayyaki daban daban na sata.

Hundeyin ya sanar da cewa, matashin yana ikirarin yana daukar aiki inda ya kan gayyato mata da zummar za a daukesu aikin soja.

Daga nan baya kasa a guiwa sai ya tafka musu sata har da kwace wa wasu motocinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel