Bazawarar da ta Sokawa Tsohon Mijinta Wuka, Ta Halaka Sabon Saurayinta
- Wata bazawara mai suna Toyin ta yanke hukuncin datse rayuwar saurayinta bayan ya datse soyayyarsu kan cewa kowa ya kama gabansa
- An gano cewa tushen rigimar shi ne karyar da Toyin tayi wa Moses kan cewa tana da ciki kuma ta dinga tatsarsa ashe ba gaskiya bane
- Ta kone shi da fetur inda ta kulle shi a daki bayan ta saka wutar, sai dai an gano cewa sokawa tsohon mijinta wuka tayi shima ya mutu
Legas - Wata bazawara mai suna Toyin ta halaka saurayinta mai suna Moses Baba-Agba a Akoro dake Badagry ta yamma a jihar Legas kan datse alakar soyayya dake tsakaninsu.
An gano cewa, saurayin ya gane cewa Toyin bata da juna biyu bayan ya tirsasata zuwa duba abinda ke cikin ta saboda tana ta karbar kudi daga wurinsa kan zata je awo a tsawon watanni.
Matar Aure Ta Kama Mijinta Na Rage Zafi Da Wata Yar Magajiya, Bidiyon Matakin da Ta Dauka Ya Girgiza Mutane
Wata ‘yar uwar mahaifiyar mamacin mai suna Pedertin Baba-Agba ta sanar da jaridar Vanguard cewa Toyin mai shekaru 24 ta sanar da Moses mai shekaru 26 cewa tana dauke da juna biyu kuma tana ta karbar kudinsa kan zata je awo har zuwa makon da ya gabata lokacin da Moses yace taje tayi hoton abinda ke cikinta a ga halin da yake ciki.
Kamar yadda tace, ta dawo inda ta sanarwa Moses cewa na’urar hoton ta lalace bayan an zo kan ta kuma hakan ne yasa mahaifiyar Moses kai ta asibiti inda aka gane cewa karya take yi. Daga nan marigayin ya datse alaka da ita, jaridar Vanguard ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daga bakin ‘yan uwan mamacin
Har ila yau, ‘yan uwan mamacin sun ce basu taba sanin cewa Moses ya rabu da ita ba.
“A daren Juma’a, Toyin ta yaudari ‘yar uwar Moses dake zama da shi inda ta kai ta gabar teku ta sha iska. Daga zuwa nan, Toyin ta sanar da ita cewa ta jira ta saboda zata dauko wasu kaya a gida.
“Toyin na isa gida ta tarar Moses na bacci. Ta watsa masa fetur tare da bankawa dakin wuta kuma ta kulle. Daga nan ta tsere da wayarsa amma ta ji rauni a kafarta saboda wutar ta laso ta.
“Da kyar Moses ya iya bude kofar ya fita wani gida neman taimako. Da farko bamu gane shi ba saboda ya kone ta yadda ba a iya gane shi.
“A haka muka kashe wutar tare da kai shi asibiti amma a safiyar Litinin yace ga garin ku. Gawarsa yanzu haka tana mutuwaren Badagry.
“Muna kira ga jama’a da su taimaka mana saboda mun gano cewa ta taba halaka tsohon mijinta a Ajara dake Badagry kuma babu abinda ya faru.
“An bibiyeta zuwa wani coci kuma an mika ta hannun ‘yan sanda. Ba mu san abinda za a yi ba har yanzu.”
- Suka bayyana.
Asali: Legit.ng