Mata Ta Kama Mijinta Na Holewa da Yar Magajiya, Bidiyon Matakin Da Ta Dauka Ya Girgiza Mutane

Mata Ta Kama Mijinta Na Holewa da Yar Magajiya, Bidiyon Matakin Da Ta Dauka Ya Girgiza Mutane

  • Wani bidiyo dake yawo a soshiyal midiya ya nuna abu mai sosa zuciya, wata mata ta gamu da Mijinta tare da 'yar hannu
  • A Bidiyon abun takaicin, matar auren ta tunkari maciya amanan amma abun mamaki mijin ya koma kokarin kare yarinyar
  • Lamarin dai ya jefa mutane cikin yanayin tausayi a Soshiyal midiya yayin da wasu suka fara faɗin yadda haka ta faru da su

Lokaci guda wata matar aure ta sauya daga yanayin farin ciki zuwa bakin ciki da takaici yayin da ta ci karo da mijinta tare da wata yar magajiya sua sharholiyarsu.

A wani bidiyo mai taɓa zuciya da aka wallafa a shafin TikTok, Matar ba ta tsaya haka nan ba ta tunkare su domin sauke musu ruwan bala'in fushinta.

Dirama tsakanin yar sharholiya da matar aure.
Mata Ta Kama Mijinta Na Holewa da Yar Magajiya, Bidiyon Matakin Da Ta Dauka Ya Girgiza Mutane Hoto: callyt3/TikTok
Asali: UGC

Abun takaicin Mijin ya koma ɓangaren abokiyar rage zafinsa inda ya rika kokarin kare ta daga duk wata kalan kokarin cutarwa ko zalunta daga matarsa.

Kara karanta wannan

Wata Dirarriyar Budurwa Ta Nemi Lambar Wani Mutumi a Gaban Matarsa, Bidiyon Abinda Ya Faru Ya Ja Hankali

Da take martani game da haka, matar abun tausayi ta koka cikin fushi da takaici a Bidiyon kuma ta nuna tsantsar mamaki da kaɗuwa da ganin halayyar da abokin rayuwarta ya nuna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duba Bidiyon anan

Yadda mutane suka maida martani a Soshiyal Midiya

@zithunywazakithi tace:

"Mutane basu san wani abu ba idan mace na shan azaɓa da wahala a hannun namiji mance wa take da kanta ballantana ta kula da kanta."

@mimiki182 ta rubuta cewa:

"Mata ina baku shawara ku daina ta da jijiyoyin wuya kan namiji wanda ba ya kallon ku da ƙima baki ɗayanku."

@tabbie.thabi yace:

"Naji maganganunki, gaskiya wannan mutumin ba shi da mutunci ko guda, duba yadda ya cire rigarsa ya sanya wa 'yar sharholiya a gaban matarsa."

@annasich0 yace:

"Ni na kasa gane meyasa take faɗa da yarinyar maimakon ta buɗa da Mai gidanta, ki tafka masa mari."

Kara karanta wannan

Cika alkawari: Tela ta saka amarya kukan dadi bayan da ta cika alkawari, ta gwangwaje ta

"Ya Hadu": Wata Budurwa Ta Bar Wani Saurayi Ya Kwanta a Jikinta, Hotonsu Ya Ja Hankali

A wani labarin kuma Wata Budurwa ta bayyana yadda wani matashin Saurayi da suka haɗu a Mota ya kishingiɗa a jikinta

Da take ba da labari a wata wallafa a shafinta, kyakkyawar budurwar ta nuna yadda abun ya mata daɗi ganin mutumin ya ɗan huta a kafaɗarta.

Tace abun sha'awar shi ne duk da ya nuna alamun gajiya da zafin gari mutumin bai tambayeta kudi ba, tace ta yi dana sanin rashin karban lambarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel