Gwamna Zulum Ya Kai Ziyarar Bazata Wasu Asibitoci, Ya Ɗauki Mataki Kan Abinda Ya Gano

Gwamna Zulum Ya Kai Ziyarar Bazata Wasu Asibitoci, Ya Ɗauki Mataki Kan Abinda Ya Gano

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum ya kai ziyarar bazata wasu Asibitoci biyu a Maiduguri bayan samun labarin babu wuta
  • Gwamnan ya tarad da majinyata a ciki duhu da daren ranar Jumu'a, ya umarci a ɗauko Dizal na gidan gwamnati a kawo Asibitocin
  • Ya kuma ba da umarnin a sanya Sola watau hanyar samar da wuta daga hasken rana a Asibitocin

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya dira wasu Asibitoci biyu dake Maiduguri ba tare da sanarwa ba da daren ranar Jumu'a, ya tarad da majinyata a cikin duhu.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa Zulum ya kai ziyarar ta ba zata ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare, ba wuta a Asibitocin sakamakon matsalar wutar Lantarkin da ake fama da ita.

Gwamna Zulum.
Gwamna Zulum Ya Kai Ziyarar Bazata Wasu Asibitoci, Ya Ɗauki Mataki Kan Abinda Ya Gano Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Gwamnan ya je Umaru Shehu Ultra Modern Hospital da kuma Fatima Ali Sheriff Maternity Hospital, dukkaninsu a yankin Bulumkutu dake ƙarƙashin Maiduguri.

Kara karanta wannan

Lauya Ya Fadi Dalili 1 da ya sa ‘Yan Sanda Janye Karar Mai 'Cin Mutuncin' Aisha Buhari

Bayanai sun nuna cewa gwamnan ya yanke zuwa Asibitocin ne kai tsaye daga Filin jirgi yayin da ya dawo daga Abuja bayan samun labarin Asibitoci na fama da rashin haske.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zulum ya gano tare da tabbatar da cewa majinyata na kwana cikin duhu ne sabida babu mai a Injinan dake Asibitocin.

An ce Asibitocin sun dogara ne da Injina saboda rashin samun wutar Lantarki tun bayan ta'asar ƙungiyar Boko Haram, wacce ta lalata kayan wutar a titin Maiduguri-Damaturu.

Abinda Zulum ya gano da matakin da ya ɗauka nan take?

Gwamnan ya tambayi shugabannin kowane Asibiti daga cikin biyun kuma ya tabbatar da rashin mam Dizal ne ya hana Injina aiki.

"Abun takaicin babu wani jami'i daga cikin jagorocin Asibitocin ko daga ma'aikatar lafiya da ya sanar da ni abinda ke faruwa. Idan har zamu samar da wuta a inda muke ba dalilin da zai sa Asibitocin mu su kasance a duhu."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Masu Yawa Kan Hanyarsu Na Zuwa Abuja

- Zulum.

Kuma nan take ya ba da umarnin a ɗauko Man Dizel ɗin da aka tanazarwa gidan gwamnati, inda gwamnan ke zaune a dawo dasu Asibitocin biyu gabanin zaman da zasu yi da ma'aikatar lafiya don nemo mafita.

Bayan wannan matakin na samar da wuta a Asibitocin biyu, Zulum ya umarci a inganta hanyar samar da wuta ta hasken rana dake Asibitin Fatima Sherrif kana a sanya Solar a Umaru Shehu Ultra Modern Hospital.

Gaskiyar Dalilin Da Yasa Ni Da Mayakana Muka Mika Wuya - Kwamandan Boko Haram, Mallam Rugurugu

A wani labarin kuma Wani tsohon Kwamandan Boko Haram Yace sa bakin gwamna Zulum na cikin abinda ya janyo ya aje makamai da mayaƙansa

A cewar Mallam Rugurugu, ya ɗauki mataki daina wannan zubar da jini bayan ya yi kansa wa'azi ya gano tabbas hanyar da ya kama ba mai kyau bace.

Haka zalika yace kalaman gwamna Zulum sun yi tasiri a kansa inda ya yanke shawarin ya fito daga jeji ya miƙa wuya don fuskantar rayuwa ta gaske.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262