Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Masu Yawa Kan Hanyarsu Na Zuwa Abuja

Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Masu Yawa Kan Hanyarsu Na Zuwa Abuja

  • Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace fasinjoji da dama a Jihar Kogi
  • Gwamnatin Kogi ta bakin mai bada shawara kan tsaro ga gwamnan jihar, Jerry Omodara ya tabbatar da afkuwar lamarin
  • Omodara ya ce gwamnati ta ankarar da jami'an tsaro kuma sun dauki matakan ganin an ceto mutanen tare da kawar da maharan

Kogi - An sace wasu fasinjoji da ba a tantance adadinsu ba a cikin wata motar bas mai wurin zaman mutum 18 a Ochadamu kan hanyar Anyigba-Itobe a karamar hukumar Ofu na jihar Kogi.

Babu tabbas ko motar cike ya ke da mutane ko akasin hakan a lokacin hada wannan rahoton.

Taswirar jihar Kogi
Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Masu Yawa Kan Hanyarsu Na Zuwa Abuja. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Ayarin Gwamnan Arewa Yana Hanyar Zuwa Kamfe

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin a wani wuri da ya yi kaurin suna wurin sace mutane, Daily Nigerian ta rahoto.

Rahotanni daga yankin ya ce bata garin masu yawa dauke da bindige sun tare motar ne suka tisa keyar fasinjojin zuwa cikin daji.

An ce motar ta fito daga kudancin Najeriya ne tana hanyar zuwa Abuja.

Mazauna kauyen sun ce jami'an tsaro da yan bijilante suna kokarin ceto wadanda aka sace din tun bayan faruwar lamarin.

Martanin Gwamnatin Jihar Kogi

Amma, kwamandan sojojin ruwa, Jerry Omodara (mai murabus), mashawarcin Gwamna Yahaya Bello kan tsaro a jihar ya tabbatar wa Daily Trust afkuwar lamarin a ranar Alhamis, yana mai cewa gwamnatin jihar tana daukan matakan da suka dace.

Ya ce gwamnatin jihar ta yi dauki matakan da suka dace domin fatattakar bata gari a yankin.

Kara karanta wannan

FG Tace Gwamnatocin Jihohi ne Suke kara Tsunduma ‘Yan Najeriya Cikin Matsanancin Talauci

Ya ce batagarin sun dawo sun fara hare-hare ne a hanyar, amma gwamnatin za ta sake zage damtse, za ta kawar da su cikin kankanin lokaci.

Ya ce:

"Mun yi yaki da su; za mu yake su; kuma za mu cigaba da yaki da su har sai mun karar da su a jihar. An ankarar da jami'an tsaro su yi abin da ya dace."

Mahara Sun Sace Babban Dan Sanda A Jihar Kwara

Wasu mahara sun sace babban dan sanda, Abdulmumini Yusuf a ranar Talata a Ogidi da ke karamar hukumar Ilorin West a jihar Kwara.

Emirate No 1, kamar yadda aka fi kiran Abdulmumini ya fada tarkon maharan ne bayan ya dawo daga aiki zai shiga gida a dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel