Kano: Bayan Sace Kayan da Ango Zai da Yaje Daurin Aure, An Sace Sadakin Amarya a Wurin Daurin Aure

Kano: Bayan Sace Kayan da Ango Zai da Yaje Daurin Aure, An Sace Sadakin Amarya a Wurin Daurin Aure

  • Jama’a sun sha matukar mamaki da al’ajabi bayan kayan da wani ango zai saka sun yi batan dabo, kasa da sa’o’i 24 kafin daurin aurensa
  • An gama mamakin faruwar al’amarin, ango ya je wurin daurin aure amma aka sake sace sadakin da zai biya na amaryarsa
  • An sake kacamewa da hayaniya tare da mamaki, iyaye dattawa ne suka shiga lamarin inda aka daura auren a bashi daga baya ango zai biya sadaki

Kano - Mazauna kwatas din Fagge dake karamar hukumar Fagge ta jihar Kano har yanzu basu farfado daga mamakin da suka shiga ba bayan abinda ya faru da wani ango kasa da sa’o’i 24 kafin daura aurensa, jaridar Leadership ta rahoto.

Taswirar jihar Kano
Kano: Bayan Sace Kayan da Ango Zai da Yaje Daurin Aure, An Sace Sadakin Amarya a Wurin Daurin Aure. Hoto daga vanguardngrnews.com
Asali: UGC

Babu zato balle tsammani aka yi wuff tare da sace kayan da ango zai saka wurin daurin aurensa tare da sadakin da zai bayar na amaryarsa.

Angon wanda ya bukaci a boye sunansa, ya duba ko sama ko kasa bai ga kayan da ya ajiye zai saka ranar auren ba a inda ya adana su.

Lamarin wanda ya faru a ranar Asabar da ta gabata ya bar angon da ‘yan uwansa cike da damuwa ganin cewa ya zage tare da tara kudi ya siya kayan amma suka bace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanda lamarin ya ritsa dashi ya garzaya caji ofis inda ya kai korafi yayin da ‘yan sandan suka fada bincike.

An sace sadaki a wurin daurin auren

Babban abun takaici wanda ya fi kayan angon shi ne sace sadakin da aka yi a wurin daurin aure. An matukar shiga mamaki bayan an gano cewa an sace sadakin amarya.

An daura aure ajalan

Har sai da iyaye suka shiga maganar sannan komai ya lafa inda aka amince a daura auren sai ango ya kawo sadaki daga baya.

Wani Abdussalam wanda ya shaida faruwar lamarin yace abun gwanin kunya kuma ya yi kira ga mutane da su kasance masu lura. Ya kara da kira ga jama’a da su kasance masu tsoron Allah tare da daina yin abinda zai bata sunan jihar Kano.

Hakazalika, wani matashi mai suna ‘Yan Bita yace lamurran biyu sun matukar bashi mamaki kuma da yana da hali tsaf zai siyawa angon sabon kayan daurin auren sannan ya bashi sadaki.

Legit.ng na tattaro muku karin bayani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel