Tashin Hankali: Ɗan Najeriya Ya Yanka Budurwarsa Har Lahira a Kasar Waje

Tashin Hankali: Ɗan Najeriya Ya Yanka Budurwarsa Har Lahira a Kasar Waje

  • 'Yan sanda a ƙasar Ghana sun yi ram da wani matashi ɗan Najeriya bisa zargin yanka budurwarsa har lahira a Accra
  • Hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje tace bata da labarin abinda ya auku amma duk wanda ya yi laifi doka ta hukunta shi
  • Ana kyautata zaton saurayain ya aikata haka ne domin asirin kuɗi da ita wanda ya saba faruwa a gida Najeriya

Accra, Ghana - Wani mutumi ɗan Najeriya da har yanzun ba'a gano bayanansa ba ya shiga komar jami'an 'yan sanda bisa zargin raba kan budurwarsa da gangar jikinta.

Wani mai amfani da shafin Facebook, Smile Baba, ya saki wani Bidiyo a shafinsa wanda ya nuna yadda aka kwamushe mutumin kuma an hangi gawar budurwar.

An kama wanda ya kashe budurwarsa.
Tashin Hankali: Ɗan Najeriya Ya Yanka Budurwarsa Har Lahira a Kasar Waje Hoto: punchng
Asali: UGC

An tattaro cewa ita ma wacce aka kashe yar asalin Najeriya ce. Baba yace lamarin ya faru ne a Anguwar Spintex, Accra babban birnin ƙasar Ghana.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Bindige Wani Fitaccen Mawaki Har Lahira a Najeriya

Ya rubuta cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abun takaice ne da yammacin nan, na ziyarci wurin da lamarin ya faru a nan Accra, Ghana inda wani matashin ɗan Najeriya ya guntule kan budurwarsa a Spintex."
"Tambayana shi ne, wake wa matasan mu maza da mata karyar cewa ana sihirin kuɗi dagaske? Mata ina jan hankalinku kusan wanda zaku amince da shi, kamalarsa a fuska ba ta wadata ba ku kiyaye."

Yayin da aka tuntuɓi mai magana da yawun hukumar 'yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abdur-Rahmam Balogun, yace hukumarsu ba ta samu rahoton lamarin ba.

Ya bayyana cewa ya zama tilas wanda ake zargi ya fuskanci hukuncin da kundin dokokin Ghana ya tanada. Yace:

"Matsayar mu ita ce duk wani ɗan Najeriya da ya aikata laifi a wata ƙasa doka ta yi aiki a kansa, babu wata rana da gwamnatin Najeriya zata yi a irin haka."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wata Matar Aure, Maryam, Ta Sheke Kishiyarta Kan Abu Daya a Arewa

"Idan kaje ƙasar wani ka aikata laifi ya kamata a bar dokar wannan ƙasa ta hukunta ka, shiyasa a ko da yaushe muke shawartan 'yan Najeriya su zama wakilai nagari."
"Ban kalli bidiyon ba kuma har yanzun ba'a kawo mana ƙorafi kan aukuwar lamarin ba."

Yadda wata matar aure ta kashe Mijinta saboda yace zai ƙara aure

A wani labarin kuma Wata matar Aure a jihar Zamfara ta halaka mai gidanta saboda ta ji labarin yana shirin ƙara aure

Matar mai suna Salamatu Shehu ta yi ajalin mijinta, Malam Shehu a ƙauyen Arfin Gero dake ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya.

An ce Magidancin ya gaya mata zai ƙara aure lamarin da ya haddasa gaddama a tsakaninsu, wata majiya tace ba ya iya biya mata bukatun saduwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel