Aisha Buhari: Takardar Tuhuma Guda Ɗaya Da Ake Wa Aminu A Kotu Ta Bayyana

Aisha Buhari: Takardar Tuhuma Guda Ɗaya Da Ake Wa Aminu A Kotu Ta Bayyana

  • Daga karshe dai takardar tuhumar da ake yi wa dalibin nan na Jami'ar Dutse, Aminu Adamu ta fito fili
  • Kamar yadda takardar tuhumar ta nuna, ana zargin Aminu da wallafa rubutu da gangan kuma karya wanda ka iya taba mutuncin Aisha Buhari
  • Lauyoyin da suka shigar da karar sun ce laifin ya saba wa sashi na 391 na dokar Penal code

A yayin da batun kama dalibin jami'ar tarayya da ke Dutse, Aminu Adamu ke cigaba daukan hankalun dai-daikun mutane da kungiyoyin, takardar karar da rundunar yan sanda suka shigar a kotu ta fito.

Aminu da Aisha
Aisha Buhari: Takardar Tuhuma Guda Ɗaya Da Ake Wa Aminu A Kotu Ta Bayyana. Hoto: Vanguard.
Asali: Facebook

An shigar da karar ne a ranar 21 ga watan Nuwamban 2022 kuma jami'an kotu suka rattaba hannu kanta a ranar 23 ga watan Nuwamba kamar yadda takardar da lauya mai kare hakkin biladama @InibeheEffiong ya wallafa a Twitter kuma Legit.ng Hausa ta gani.

Kara karanta wannan

Kame dalibi kan zagin matar Buhari: Dalibai sun fadi matakin da za su dauka kan Aisha Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tuhumi Aminu Adamu ne da laifi guda daya kacal na yin amfani da shafinsa na Twitter mai suna @aminullahie ya wallafa rubutu na cewa 'Su Mama anchi kudi talakawa ankoshi' tare da hoton Mai girma Aisha Buhari.

Aisha Buhari: Tuhumar da ake yi wa Aminu Ahmad

Lauyoyin da suka da ya shigar da karar sune James Idachaba da Fidelis Ogbobe kamar yadda takardar ta nuna.

Idachaba ya ce wallafar da wanda ake zargin ya yi wanda ya san karya ne zai iya shafar mutuncin matar shugaban kasa.

Ya kuma ce hakan laifi ne karkashin sashi na 391 na dokar Penal Code.

Yan Najeriya da kungiyoyi da dama musamman a soshiyal midiya suna ta maganganu ne kira da cewa a saki Aminu.

Kungiyar daliban Najeriya za ta yi zanga-zanga kan tsare Aminu Muhammad

Kara karanta wannan

Badakalar N260m: Kotu Ta Yankewa Tsohon Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Gusau shekaru 35 A Gidan Dan kande

Shugaban kungiyar daliban Najeriya, NANS, ta ce za ta shirya zanga-zangar lumana a fadin kasar domin neman a sako dan uwansu daliban jami'ar FUD, Aminu Muhammad da ake tsare da shi kan zargi cin mutuncin Aisha Buhari.

Usman Barambu, shugaban NANs ne ya fitar da wannan sanarwar a ranar Alhamis, yana mai bayyana fara zanga-zangar don nuna kin amincewarsu da tsare Aminu.

Ya ce kungiyar za ta fara zanga-zangar ne a ranar 5 ga watan Disamba a dukkan sassar kasar muddin ba a saki Aminu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel