Zargin Cin Hanci Da Rashawa Kotu Ta Daure Tsohon Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Gusau

Zargin Cin Hanci Da Rashawa Kotu Ta Daure Tsohon Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Gusau

  • Kotu ta tura tsohon shugaban jami'ar tarayya ta Gusau Farfesa Graba gidan yari na tsawon shekaru 35
  • Ba Kasafai aka fiye samun saba lamba a tsakanin malaman jami'oi ba musamman ma batun cin hanci da rashawa
  • Hukumar EFCC da takwararta ta ICPC na da hurumi ko damar bincikar kananu da manyan ma'aikatan gwamnati

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta samu nasara kan karar da ta shigar akan Farfesa Magaji Garba, tsohon Shugaban Jami’ar Tarayya Gusau.

Mai shari’a Maryam Hassan Aliyu ta babbar kotun birnin tarayya, ta ce an samu wanda ake tuhumar ne da laifuffuka biyar da suka hada da samun kudi ta hanyar haram, halatta dukiyar haram da sauransu.

Mai shar'ar ta ce a dalilin haka kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 35 a gidan dan kande dan gyara hali kamar yadda hukumar ta wallafa a shafin ta na Twitter

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar EFCC dai ta gurfanar da Farfesa garba ne tun a ranar 12 ga Oktoba, 2021, bisa zarginsa da karbar wasu kudade daga hannun wani dan kwangila bisa zargin ba shi kwangilar Naira biliyan 3.

Shugaban
Zargin Cin Hanci Da Rashawa Kotu Ta Daure Tsohon Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Gusau Hoto: Twitter EFCC
Asali: Twitter

Wannan batu kuwa ya sabawa sashe na 1 (1) (a) kuma hukunchin shi na karkashin sashe na 1 (3) na laifukan dake karkashin dokar 2006.

A Nigeria dai ba kasafai aka fiye jin shugabannin jami'oi na fadawa komar hukumar EFCC ba, sabida yadda ake ganin sune na gaba-gaba, wajen ganin an inganta hakar ilimi, lafiya noma da dai sauran batutuwan da suka shafi 'yan kasa dan inganta rayuwarsu.

ASUU Tayi Barazanar Yajin Aikin Da Ba'a Taba Yi Ba

A wani labarin kuma, kungiyar malaman jami'oi ta ASUU ta ce yan Nigeria su kwan da shirin sabon shirin su na tafiya yajin aikin da ba;'a taba ganin irinsa ba a Kasar. Sabida yadda gwamnati ta hana su albashin wata takwas.

Kara karanta wannan

Daraktoci A Ma'aikatu rirnsu CBn da NCC Sunfi Buhari Daukar Albashi Duk Wata

Wannan na zuwa kwana guda bayan da wasu daga cikin malamn suka fara samun albashinsu na wata daya maimakon na watanni takwas da suke bi. rahotan Daily Trust ya rawaito cewa malamn basu ji dadin lamarin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel