Yadda Wani Dalibi Dan Jami'ar Al-Azhar Ya Rasu A Gidan Sa Yana Sujjada

Yadda Wani Dalibi Dan Jami'ar Al-Azhar Ya Rasu A Gidan Sa Yana Sujjada

  • Ba Kasafai dai aka fiye samun labaran Mutum Ya mutu yana ibada ba, ko kuma wani abu na bautawa Allah
  • Yawanci Mutane Na Ganin Mutuwa a lokacin Ibada wata hanaya ce ta nuna yadda mutum zai hadu da Allah lafiya ko kuma baiwa
  • Ana Alakanta Mutuwar mutane bayin Allah da wani aikin alheri da aska ga sun aikata a karshen rayuwarsu ko kuma lokacin mutuwa

Egypt: Ahmed El-Sharkawy ya shafe kwanaki uku ba tare da an gan shi a tsangayar koyar da ilmin likitanci ta Jami'ar Al-Azhar wacce ke da reshen a Assiutba inda yake karantar likitanci.

Abokansa wanda suke karatu tare sun ziyarci gidansa da ke rukuni na biyu na ginin gidajen jami'ar, inda suka tarar da kofarsa a rufe, don haka suka sanar da 'yan sanda, inda suka bude kofar da karfi.

Wani Dalibi
Yadda Wani Dalibi Dan Jami'ar Al-Azhar Ya Rasu A Gidan Sa Yana Sujjada Hoto: Dr Muhammad Salah
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr Muhammad Salah ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

"An sami Ahmed El-Sharkawy akan sallayar sallah yana sujada kuma wanda daga baya aka tabbatar ya rasu a haka
Ahmed El-Sharkawy, dalibi a shekara ta shida a tsangayar koyan aikin likitanci na Jami'ar Al-Azhar. binciken da likitoci sukai ya nuna Ya rasu ne kwanaki kadan ba da jimawa ba."

Ladduban da ake bi Allah ya Amsa Addu'a

Hadisin manzon Allha S.A.W wanda matarsa ta rawaito Ummu Sulaim Allah ya ƙada mata yarda tace :

tace naje wajen manzon rahma na tambayashe wacce kalma zan roki Allah da ita kuma ya biya min sai Manzon Rahma Yace : kice (Subhanallah) da (Alhamdulillah) da (Allahu Akbar) duk sau sau goma, sannan sai ƙi roƙi buƙatar ki, Allah biya miki" Imamu Ahmad: 11797

daga abin da aka rawaito a wannan hadisin da ke sama zaa'a fahimci cewa abubuwa masu sauki kan sa Allah ya Amshi addu'r Bayi tare da biya musu bukatu.

Akwai Hanyoyi Masu Yawa Da aka rawaito na Amsar Addu'a, Legit.ng Hausa ta tattaro wasu hanyoyi guda Saba'in da hudu da mallam Aminu Daurawa Ya Kawo na Amsar addurar bayi,

idan kana so kasan sn su ko karanta su sa ka danna Nan dan samun su da samun wasu batutuwan masu kama da su a shafin legit.ng hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel